Back

An kashe jami’in Hukumar Kwastam a Katsina kan harbin fasinja

Wasu fasinjojin wata babbar mota sun kashe jami’in Kwastam a hanyar Katsina zuwa Dankama a ƙaramar hukumar Kaita a jihar.

An ruwaito cewa lamarin ya faru ne da safiyar Laraba a ƙauyen Gamjin Makaho da ke kan hanyar Dankama.

Majiyoyi sun ce motar tana jigilar mutane zuwa garin Dankama ne lokacin da jami’an Kwastam suka yi ƙoƙarin tsayar da ita, amma direban ya ƙi tsayawa.

An ce ɗaya daga cikin jami’an Kwastam ɗin ne ya harbi ɗaya daga cikin fasinjojin a kugu.

Daga ƙarshe direban babbar motar ya tsaya, fasinjojin suka sauka domin fuskantar jami’an Kwastam, suka hau kan wanda ya yi harbin.

Rahotanni sun bayyana cewa, a ƙarshe fasinjojin sun kashe jami’in Kwastam ɗin, wanda ba a iya tantance sunansa da matsayinsa har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton ba.

Wanda aka kashe mai suna Bashir Na-Buzuwa, an ce shi ma ya mutu ne sakamakon harbin da aka yi masa.

Marigayi Na-Buzuwa, wanda aka ce yana da kimanin shekara 27 kuma ɗan asalin garin Doro ne a ƙaramar hukumar Bindawa, mazaunin Zanguna ne a cikin birnin Katsina.

Da aka tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Kwastam a Jihar Katsina, SC Tahir Balarabe, ya ce hukumar za ta fitar da sanarwa kan lamarin, inda ya ƙara da cewa suna ƙoƙarin ɗauko gawar abokin aikin nasu.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?