Back

An kashe malamin Jami’ar Maiduguri da wuƙa a ofishin sa

Marigayin, Dakta Kamar Abdulkadir

An daɓa wa wani malami kuma Jami’in Jarabawa a Jami’ar Maiduguri, Dakta Kamar Abdulkadir, wuƙa a ofishinsa ranar Lahadi.

Marigayin na Sashen Ilimin Lafiyar Jiki ne.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Jami’ar, Farfesa Danjuma Gambo, ya ce an kashe malamin ne a yammacin Lahadi.

Ya ce ba a kama kowa ba amma ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro sun fara bincike kan lamarin.

An ruwaito cewa, Abdulkadir yana ofishin sa ne yana aiki lokacin da maharan suka kashe shi.

Da aka tambaye shi ko kisan nasa na da alaƙa da muƙamin jami’in jarrabawar, kakakin ya ce, “Hukumar Jami’ar ta ba ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro damar kammala bincikensu, kuma tabbas za su bayar da rahoto kan haƙiƙanin abin da ya faru da kuma dalilin da ya sa.”

Wani malami a jami’ar ya ce marigayin ya yi amfani da damar hutun Ista wajen kammala wasu ayyuka a kan teburinsa lokacin da maharan suka kutsa kai suka kashe shi.

Ya ƙara da cewa “an kashe shi da wuƙa da guduma, aka bar shi a cikin tafkin jininsa. Sun kuma tsere da motarsa ​​da wasu kayayyaki masu daraja. Duk da haka, mutane da yawa suna danganta kisan da muƙamin sa a matsayin jami’in jarrabawa.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?