Aƙalla mutane 3 ne aka tabbatar da mutuwarsu, wasu 3 kuma aka raunata a wani harin da aka kai da tsakar dare a wasu ƙauyuka biyu a ƙananan hukumomin Mangu da Bokkos na Jihar Filato, inji Kakakin rundunar tsaro, Manjo Samson Zhakom.
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, yana mai cewa abin Allah wadai ne.
A wata sanarwa da kakakinsa, Gyang Bere, ya sanyawa hannu, Mutfwang ya ce hare-haren da suka faru a daren Juma’a abin takaici ne kuma ba za a amince da su ba.
Da yake tabbatar da harin ga jaridar Blueprint, jami’in yaɗa labarai na Operation Safe Haven (OPSH), Manjo Samson Zhakom, ya ce mutane 3 ne suka rasa rayukansu a hare-haren biyu.
“A jiya an samu matsalar tsaro a ƙaramar hukumar Bokkos da Mangu ta Jihar Filato. Sai dai martanin da sojojin OPSH suka bayar a kan lokaci ya daƙile lamarin.
“A Mandung Mushu da ke ƙaramar hukumar Bokkos, mutane 3 ne suka raunata yayin harin kuma an kai su asibiti, daga baya 2 daga cikin waɗanda suka raunata suka mutu.
“A Kopnalle da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Mangu ta Jihar Filato, an kashe mutum 1 na yankin yayin da 2 suka raunata.
“An ƙona wani coci da wani gida amma sojojin sun kashe wutar. Jimillar mutane 3 ne suka mutu sannan 3 suka raunata,” inji Manjo Samson Zhakom.