Back

An kashe mutum daya, Mutane da dama sun rasa matsugunin su, yayin da ake zargin makiyaya sun kai hari a Jihar Yobe

Rahotanni sun nuna cewa an kashe mutum guda tare da rabauta wasu da dama gidajen su a yayin da wasu da ake zargin makiyaya ne suka kai hari kauyen Gurjaji da ke karamar hukumar Fika a jihar Yobe.

Maharan sun afkawa al’umma da baka da kibau da sanyin safiyar Talata inda suka yi harbe-harba tare da kona gidaje da shaguna.

Wannan mummunan abu da ya faru ya tilastawa mazauna kauyukan da dama gudu zuwa kauyukan da ke kusa domin tsira da rayukan su.

Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA), Mohammed Goje ya tabbatar da faruwar lamarin a wani sako da ya wallafa ta shafin shi na Facebook da aka tabbatar.

“Bisa binciken, adadin gidaje dari da ar’ba’in da shida, da mutane sama da dubu daya ya shafa, wadanda suka hada da mata masu juna biyu da masu shayarwa, yara, nakasassu da tsoffi da suka rasa matsugunan su, suka kuma ruga zuwa yankunan Maluri, Garin Ari, Dibbol, Bulaburin, da Bulaburin. Al’ummar Fika.

“An lalata dukiyoyi na miliyoyin Naira na sama da kashi tamanin da biyar na al’ummar garin.” Inji shi 

Yace, “in cikin bakin cikin, an kashe mutum 1, kurma mai shekaru 50, da kibiya a kirjin shi, wani mutum Kuma ya samu munanan raunuka.”

Ya ce kamar yadda Gwamna Buni ta ba da umarni, a halin yanzu SEMA na kara zage damtse wajen tallafa wa wadanda abin ya shafa, yayin da ake ci gaba da tsugunar da su da kuma mayar da su gida.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?