Back

An kashe mutum huɗu a turmutsitsin rarraba zakka a Bauchi

Mutane 4 ne suka rasa rayukansu a wani turmutsitsi da ya ɓarke a lokacin da ake gudanar da zakka ga talakawa a jihar Bauchi.

Rikicin ya afku ne a shalkwatar kamfanin Shafa Holdings plc dake kan titin Jos, ranar Lahadi da misalin ƙarfe 12 na rana.

Wata yarinya mai suna Naima Abdullahi mai shekaru 17 a yanzu haka tana jinya a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar ‘yan sandan, Ahmed Wakili, ne ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma bayar da tabbacin cewa a halin yanzu lamarin ya daidaita.

Ya bayyana cewa ‘yan sandan sun yi gaggawar ɗaukar matakin ne da jin labarin, kuma Kwamishinan ‘Yan Sandan ya ƙarfafawa jama’a da su kasance cikin hayyacinsu.

Lokacin da suka ziyarci wurin, an tarwatsa jama’a, kuma an ajiye motocin ‘yan sanda a yankin. Duk da haka, wasu mata har yanzu suna jira a waje suna sa ran za a ci gaba da raba zakkar.

Kawo yanzu dai babu wata sanarwa da kamfanin ya fitar.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?