Back

An kashe wasu mazauna Delta yayin da fusatattun sojoji suka ƙona gidaje a Bayelsa

Biyo bayan kashe hafsoshi da sojoji 16 da aka yi a makon da ya gabata a yankin Okuama da ke jihar Delta, sojojin Nijeriya sun kai farmaki kan al’ummar Igbomotoru da ke ƙaramar hukumar Ijaw ta Kudancin jihar Bayelsa, inda suka yi ta lalata gidaje tare da kashe kimanin mutane 11.

Sojoji a cikin kwale-kwale guda biyar sun afka cikin al’ummar yankin, inda suka rusa gidajen da ake zargin maɓoyar wani shugaban ‘yan bindiga ne da aka ce yana da hannu wajen kashe sojojin da suka je aikin ceto a Delta.

An ruwaito yadda aka kashe Kwamandan Sojoji, Manjo biyu, Kyaftin ɗaya da sojoji 12 a Okuama.

Hafsoshin da sojojin da suka mutu na Bataliya ta 181 ne a ƙaramar hukumar Bomadi ta jihar Delta.

Babban Hafsan Hafsoshin Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa, ne ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa tare da cafke waɗanda ke da hannu a wannan aika-aika.

Kwanaki bayan umarnin, mazauna yankin Okuama sun gudu zuwa Ughelli maƙwabciyarta saboda fargabar ramuwar gayya daga sojoji.

An ƙona gidaje a Okuama a ƙarshen mako kuma bayan haka ne sojoji suka kai hari maƙwabciyar Bayelsa.

Wata majiya ta ce nan take sojojin suka afkawa al’ummar Bayelsa, inda suka buɗe wuta kan wasu mazauna wurin da suke shaƙatawa a gaɓar teku kafin su ci gaba da ƙona gine-gine uku da ake zargin maɓoyar shugaban ‘yan ta’addan ne.

Ya ce al’ummar yankin sun samu nasarar samo gawarwaki 11 daga harin, yayin da ake ci gaba da neman wasu har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

A cewarsa, “Mamayar da sojoji suka yi ya shafi mutane matuƙa. An yi asarar rayuka, an lalata dukiyoyi. Ko bayan harin, na tabbata cewa rayuwa a cikin al’ummar ba za ta kasance iri ɗaya ba.

“A ƙarshen makon nan ne aka shirya yin jana’izar wani kawuna da ya rasu. Mun biya kuɗin abinci, abin sha, kiɗa, kwale-kwale da rumfa. Kuma yanzu saboda wannan, ba za a iya yin jana’izar ba.

“Wasu daga cikin mutanen da muka biya kuɗi suna cewa idan ranar ta canza, sai mun biya ƙarin kuɗi. Shin wannan ba babbar asara ba ce? Don haka sai mu fara neman ƙarin kuɗi, idan har za a samu zaman lafiya a cikin al’ummar kenan.

“Ina kira ga Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jiha da su gaggauta sa baki a wannan lamarin. Ba mu da hannu a duk abin da ya faru a Jihar Delta. Ya kamata ƙasashen duniya su kawo mana agaji.”

Da aka tuntuɓi kakakin hedikwatar Operation Delta Safe (OPDS) ta wayar tarho, Manjo Adenegan Ojo, ya katse kiran bayan ya ji cewa ɗan jarida ne ya kira. Sai dai ya ƙi amsa kiran waya da suka biyo baya.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?