Back

An Kashe ‘Yar Shekaru Casa’in Tare Da Jikar Ta A Daura

Wata mata ‘yar shekara 90 mai suna Hajiya Amina tare da jikar ta Bilkisu ‘yar shekara 23, an yi musu kisan gilla a unguwar Tudun Wada da ke garin Daura a jihar Katsina a ranar Alhamis.

Mummunan lamarin ya faru ne a gidan waɗanda abin ya shafa a bayan Tashar Kudu a cikin garin Daura.

Rahotanni sun bayyana cewa, an shaƙe ‘yar shekara 90 ɗin ne yayin da aka yanka jikar ta.

Wani mazaunin garin Daura ya kuma shaida cewa maharan sun yage cikin jikar tare da cire mata ƙoda, zargin da wannan jaridar ba ta iya tantancewa kai tsaye ba kenan.

Wannan jarida ta tattaro cewa ba da daɗewa ba, wasu matasa sun yi fashi a gidan waɗanda abin ya shafa suka tafi da talabijin ɗin su na plasma.

Marigayiyar ta kai rahoton faruwar lamarin ga ‘yan sanda bayan da Hakan ya faru, ana ci gaba da gudanar da bincike a lokacin da aka kashe waɗanda abin ya shafa.

Daga baya an gano talabijin din kuma Bincike ne kawai zai nuna ko waɗanda suka saci talabijin suna da alaƙa kai tsaye ko a kaikaice da kisan.

Gwamna Dikko Umar Radda na jihar Katsina ya jajantawa iyalan mamatan da kuma masarautar Daura bisa wannan lamari da ya faru.

Da aka tuntuɓi Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsinan, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce akwai abin tambaya a cikakkun bayanan.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?