Back

An kuɓutar da ɗaliban jami’a da masu bautar ƙasa da aka sace a Zamfara

Ragowar ma’aikata da ɗaliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau a Jihar Zamfara da aka sace a ranar 22 ga Satumba, 2023, sun samu ‘yanci.

Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki gidajen kwanan ɗalibai a unguwar Sabon-Gida da ke ƙaramar hukumar Bungudu a Jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da ɗalibai sama da 20, yawancinsu mata.

Bayan ƙoƙarin da hukumomin jami’ar da ‘yan uwa suka yi, an sako wasu daga cikin waɗanda aka kama bayan watanni, amma 23 suna hannun ‘yan bindigan.

Sai dai wasu majiyoyi sun shaida cewa jami’an tsaro sun ceto sauran ɗaliban a ranar Lahadi.

“An sako su ne a Kuncin Kalgo da ke ƙaramar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara kuma aka miƙa su ga jami’an gwamnati ranar Lahadi. Jimillar mutane 23 ne gaba ɗaya,” inji wata majiya da ke da masaniyar ci gaban kai tsaye.

Majiyar ta ƙara da cewa an kuɓutar da wasu daga cikin masu bautar ƙasa (NYSC) da aka sace a Jihar Sokoto.

Jihar Zamfara dai na ɗaya daga cikin jihohin da rikicin ya shafa a yaƙin da ake yi da ‘yan bindigar da suka addabi mazauna yankin Arewa maso Yamma.

A lokacin da ya nemi ganawa da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a Aso Rock a watan da ya gabata, Gwamna Dauda Lawal na Zamfara ya ce an yi wa jiharsa kawanya.

“An kai hare-hare da dama a wasu ƙananan hukumomin. Ina jin a matsayina na gwamna, ya kamata in sanar da mai girma Shugaban Ƙasa, wanda ya ji daɗin tattaunawar da muka yi, kuma muna neman ƙarin jami’an soji da kuma kayan aikin da za su yi aiki yadda ya kamata da kuma magance yanayin tsaron”.

“Zamfara ta zama cibiyar ‘yan ta’adda, kuma idan ba a yi wani abu a Jihar Zamfara ba, ba na jin za mu iya magance matsalar a Arewacin Nijeriya baki ɗaya. Yawancin samari ko ‘yan matan da aka sace a Jihar Kaduna, sun ƙare ne a Jihar Zamfara wanda bai dace da mu ba, don haka muna yin duk abin da zai sa mu canza labarin kuma wannan na ɗaya daga cikin dalilan da ya sa na zo ganin Shugaban Ƙasa a yau.

“Don haka ne na zo nan a yau na sanar da Shugaban Ƙasa kuma ya ba ni tabbacin cewa za a yi wani abu mai tsauri don shawo kan lamarin da wuri,” kamar yadda ya shaida wa manema labarai na gidan gwamnatin jihar.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?