Back

An kuɓutar da mutane 386 daga dajin Sambisa shekaru 10 bayan sace su – Sojoji

Aƙalla mutane 386 ne akasari mata da ƙananan yara sojoji suka ceto a dajin Sambisa shekaru goma bayan sace su.

Muƙaddashin GOC 7 Division, Birgadiya Janar AGL Haruna, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a wajen dajin Sambisa a ƙaramar hukumar Konduga bayan ya karɓi baƙuncin sojojin da suka gudanar da aikin na kwanaki 10.

Haruna ya ce, farmakin da aka yi wa laƙabi da “Operation Desert Sanity 111” shi ne share dajin Sambisa daga dukkan nau’o’in ‘yan ta’adda da suka rage tare da baiwa masu son miƙa wuya damar miƙa wuya.

“Ƙoƙarin da muke yi shi ne mu tabbatar da cewa mun kawar da ragowar ‘yan ta’adda a Sambisa tare da baiwa masu son miƙa wuya damar miƙa wuya.

“Da wannan aiki, muna sa ran da yawa daga cikinsu za su miƙa wuya kamar yadda suka fara.

“Mun kuma ceto wasu fararen hula; Ya zuwa jiya mun ceto 386 kuma na tabbata adadin zai ƙaru zuwa yau,” inji Haruna.

GOC wanda ya yi wa sojojin jawabi kan saƙon Babban Hafsan Sojin Kasar, ya yaba da ƙwazon da suka nuna a lokacin aikin, ya kuma buƙace su da su ci gaba da gudanar da aikin.

Wasu daga cikin waɗanda aka ceto da suka yi magana, sun ce shekaru 10 da suka gabata aka yi garkuwa da su.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, sojojin na 21 Special Armored Brigade, 26 Task Force Brigade, da Runduna ta Musamman 199 ne suka yi aikin.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?