Back

An mayar da Sarki Sanusi ne don amfanin jihar, inji Gwamnatin Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta ce an mayar da Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II ne domin amfanin jihar.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin ta bayyana cewa jihar na cikin kwanciyar hankali duk da tarzomar da wasu ɓata gari ke yi.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Baba Halilu Dantiye, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, ya ce gwamnati ta lura da rahotannin da wasu kafafen yaɗa labarai suka yi kan “mummunar zanga-zangar da aka yi ta yi a wasu sassan jihar dangane da rushe masarautu huɗu da mayar da Sunusi a matsayin Sarkin Kano.”

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Bisa la’akari da halin da jihar ke ciki a halin yanzu, buƙatar kawar da fargabar da jama’a ke ciki bayan rahotannin, a tabbatar musu da jajircewar gwamnati wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin su da kuma daidaita al’amura ya zama dole don bayyana kuskuren dake cikin rahotannin kafofin watsa labaru da kuma gabatar da haƙiƙanin halin da ake ciki.

“Saɓanin rahotannin kafafen yaɗa labarai, babu wata zanga-zanga da ta yaɗu a jihar Kano. Yayin da gwamnati ke sane da abubuwan da ƙananan yara da miyagu da ‘yan daba da aka ɗauka haya suka yi a yankuna kaɗan, hakan ba ya nuna halin da ake ciki a duka jihar. Waɗannan mutane marasa kishin ƙasa da aka ɗauka hayar, suna da burin tada zaune tsaye ne kawai domin amfanin kansu da kuma son kai na masu biyansu. Mafi akasarin al’ummar Jihar Kano sun nuna halin ko in kula da kuma fahimtar haƙiƙanin matakin da gwamnatin jihar ta ɗauka.

“Haka kuma ya kamata a nanata cewa matakin da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ɗauka na rushe masarautun bisa doka tare da maido da Sarkin Kano na 14 ya zo ne bayan an yi nazari sosai kan maslahar jihar. Gagarumin kaso na jama’ar da suka fahimci da kuma daraja fa’idar da ke tattare da tsarin masarauta guda sun yi marhabin da matakin.”

Gwamnatin ta ci gaba da cewa, wasu ‘yan siyasa ne ke amfani da lamarin domin haifar da hargitsi da tashe-tashen hankula, inda ta ƙara da cewa waɗannan mutane suna amfani da kafafen yaɗa labarai wajen yaɗa labaran ƙarya da tada hankalin jama’a.

“Ayyukan da suke yi da na wakilansu ba su wakiltar ainihin ra’ayin ‘yan jihar Kano, a maimakon haka, munanan manufofin son kai ne ke tafiyar da su.

“Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta tsaya tsayin daka wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Kano. Gwamnati ba za ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta ba na ɗaukar dukkan matakan da suka dace don ganin an kiyaye doka da oda tare da kare haƙƙin ‘yan jihar,” inji ta.

Gwamnati ta buƙaci jama’a da su yi watsi da “rahotannin kafafen yaɗa labarai na wuce gona da iri tare da goyan bayan ƙoƙarin gwamnati na samar da jiha mai haɗin kai yayin da ta yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su yi aikin jarida yadda ya dace tare da tantance gaskiya kafin buga duk wani rahoto da ke da yuwuwar haifar da tashin hankali.”

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf na ci gaba da jajircewa wajen ganin ci gaban jihar tare da yin kira ga ‘yan jihar da su ba da haɗin kai a kan hakan.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?