Aƙalla makarantu 723 ne aka ruwaito an rufe su a jihohi tara a faɗin ƙasar nan sakamakon rashin tsaro da mamaye harabar makarantar da wasu jami’an gwamnati da waɗanda ba na gwamnati ba, da ‘Yan Gudun Hijira (IDPs), tare da ambaliyar ruwa da ta kai ga cikas ga aikin koyarwa da koyo a makarantun da abin ya shafa.
A cewar Bayanan Safe School na Asusun Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, (Satumba 2023), jihohin da abin ya shafa sun haɗa da Adamawa, Benue, Borno, Imo, Katsina, Kebbi, Sokoto, Yobe da Zamfara.
Binciken ya nuna cewa an rufe makarantu 26 a jihar Adamawa, Benue kuma an rufe makarantu 28, Borno 72, Imo 62, Katsina 61, Kebbi 68, Sokoto 115, Yobe 15, da Zamfara 276.
Bayanai sun nuna cewa, jami’an gwamnati sun mamaye makarantu bakwai a jihar Adamawa, 11 a Binuwai, 36 a Borno, ɗaya a Imo, bakwai a Katsina, ɗaya a Yobe da kuma 22 a jihar Zamfara.
A halin da ake ciki kuma, an ce wasu da ba jami’an gwamnati ba sun ƙwace makarantu biyu a jihar Borno, 45 a Imo da kuma 134 a jihar Zamfara.
Bayanai sun nuna cewa makarantu tara ne aka rufe sakamakon ambaliyar ruwa a jihar Adamawa, 19 a Borno, 16 a Imo, 54 a Katsina, 24 a Kebbi, 109 a Sokoto, 14 a Yobe da kuma 58 a jihar Zamfara.
Har ila yau, Jihohi shida na Adamawa, Benue, Borno, Kebbi, Sokoto, da Zamfara suna da 154 na makarantunsu da ‘Yan Gudun Hijira, IDPs, suka mamaye.
A cewar bayanan, adadin ‘yan gudun hijirar da suka mamaye makarantu a Adamawa ya kai 10, Benue 17, Borno 15, Kebbi 44, Sokoto 6, Zamfara 62.
Da take magana kan mahimmancin ilimi ga yaro, Jami’ar Sadarwa Ta UNICEF, Ofishin Enugu, Dokta Ijeoma Onuoha-Ogwe ta ce “ilimi hakki ne na kowane yaro, bai kamata ya faru da yaro a Najeriya a matsayin dama ba amma a matsayin hakki.”