Back

An saki yaran makarantar Kuriga, inji Gwamnan jihar Kaduna

Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani

Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa an sako yaran makarantar Kuriga daga hannun waɗanda suka sace su.

Gwamna Sani ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu tare da rabawa a shafin sa na X.

A cikin sanarwar, Sani ya yaba da ƙoƙarin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, Mai Ba wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, da sojojin Nijeriya da ɗaukacin ‘yan Nijeriya kan irin addu’o’in da suke yi.

Sanarwar Uba Sani ta ce: “Da sunan Allah Mai Rahama, Mai jin ƙai, ina so in sanar da cewa an sako yaranmu na makarantar Kuriga.

“Muna godiya ta musamman ga mai girma shugaban mu, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, kan yadda ya ba da fifiko kan tsaron ‘yan Nijeriya da kuma tabbatar da ganin an sako yaran makarantar Kuriga da aka sace ba tare da wani lahani ba.

“Yayin da yaran makarantar suke hannun masu garkuwan, na yi magana da Shugaban Ƙasa sau da yawa. Ya yi baƙin ciki tare damu, ya lallashe mu kuma ya yi aiki dare da rana tare da mu don tabbatar da dawowar yaran lafiya.

“Dole ne kuma a yi magana ta musamman kan ɗan uwanmu, Mai ba da Shawara kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu bisa jagoranci nagari. Na sha kwana babu barci tare da Malam Ribadu muna dabaru tare da daidaita ayyukan hukumomin tsaro, wanda a ƙarshe ya haifar da wannan sakamako mai nasara.

“Sojojin Nijeriya kuma sun cancanci yabo na musamman saboda nuna cewa tare da jarumta da jajircewa, za a iya rage masu aikata laifuka tare da dawo da tsaro a cikin al’ummominmu.

“Muna kuma gode wa ɗaukacin ‘yan Nijeriya da suka yi addu’a domin Allah Ya mayar da yaran makarantar lafiya. Lallai wannan ranar farin ciki ce. Muna godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki.”

Ba a bayar da lambar adadin yaran makarantar da aka saki ba.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?