Shugaban Ƙasa Bola Tinubu zai ziyarci jihar Neja a ranar Litinin mai zuwa, kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana.
Da take zantawa da manema labarai a Minna ranar Lahadi, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Dabaru a jihar, Binta Mamman, ta ce gwamnati ta kammala shirye-shirye domin tabbatar da ziyarar Shugaban Ƙasar cikin sauƙi.
Yanzu dai za a sauya sunan filin jirgin saman Minna mai sunan Abubakar Iman da sunan Shugaba Tinubu, inji kwamishinan.
Ta ce Shugaba Tinubu zai ziyarci jihar ne domin ƙaddamar da kayan aikin noma na biliyoyin naira da gwamnatin jihar ta sawo da sauran su.
A cewarta, an samar da dukkan matakan da suka dace don ganin cewa Shugaban ya kai ziyarar ba tare da tangarɗa ba.
Kwamishinan ta ƙara da cewa, sauran ayyukan da za a ƙaddamar sun haɗa da ɗakin saukar alhazai a tashar jirgin da za a gyara.
A nasa ɓangaren, Kwamishinan Noma, Bawa Bosso, ya jaddada ƙudirin gwamnatin Gwamna Umaru Bago na tabbatar da samar da abinci a ƙasar nan, don haka za a ƙaddamar da injinan noma.
Ya ce gwamnan ya samar da taraktoci 500 cikin 10,000, yayin da injinan noma 200 ke nan a ƙasa cikin 1,000 da aka yi niyya.
Sai dai har yanzu injinan shuka ba su iso ba kasancewar an ajiye dukkansu a filin jirgin Minna domin fara aikin da aka shirya yi a ranar Litinin.
A halin da ake ciki, Mai ba da Shawara na Musamman kan Harkokin Mulki da Garambuwal, Isah Adamu, ya ce shugaban ƙasar zai kuma ƙaddamar da kayan aikin gona da aka sawo tare da aza harsashin ɗakin saukar alhazai a filin jirgin kafin shugaban ya dawo Abuja.