Back

An tsaurara matakan tsaro a kotun koli yau saboda shari’ar Shugaban ‘yan a ware ta Biafara, Nnamdi Kanu

Jami’an harkokin tsaro na kasa DSS sun tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen babbar kotun tarayya da ke Abuja, yayin da ake sa ran kotun za ta fara shari’ar shugaban masu fafutukar ballewa daga Najeriya su kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu a yau.

An dakatar da maganar ne a wasu lokuta da suka wuce bayan kotun daukaka kara ta sallami Kanu tare da wanke shi a watan goma da ya wuce.

Kotun daukaka karar ta kuma bayyana cewa ba a bi doka da ka’id ba sace Kanu da gwamnatin Najeriya ta yi daga ƙasar Kenya zuwa Najeriya, kotun ta kuma soke tuhume-tuhumen ta’addancin da gwamnatin tarayya ke yi masa.

Sai dai gwamnatin tarayyar ta daukaka kara zuwa kotun koli kan wancan hukuncin da aka yanke.

Kotun kolin da ta yanke hukunci a ranar Sha biyar ga watan goma na shekarar bara, ta bayar da umarnin ci gaba da shari’ar Kanu bisa zargin ta’addanci.

Kanu yana tsare a hannun DSS tun watan shida na shekara ta dubu biyu da ashirin da daya lokacin da aka dawo da shi daga ƙasar Kenya zuwa Najeriya.

Kafin shiga harabar kotun, an yi bincike – bincike wa ’yan jarida da masu kara da ma’aikatan kotun shingayen binciken ababen hawa hudu, tun daga hanyar da ta isa zuwa ma’aikatar shari’a.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?