Back

An tsinci gawar basarake da aka sace a Bauchi

An kashe hakimin ƙauyen Riruwai da ke gundumar Lame a masarautar Bauchi a ƙaramar hukumar Toro a jihar Bauchi, Alhaji Garba Badamasi.

An ruwaito cewa tun da farko wasu ‘yan bindiga ne da suka kai hari yankinsa suka yi garkuwa da basaraken ƙauyen a ranar Juma’a, 15 ga Maris, 2024.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce ‘yan bindigar sun shiga fadar marigayin kai tsaye inda suka yi awon gaba da shi.

An ce marigayin ya yi kwana ɗaya a tsare kafin a kashe shi tare da jefar da gawarsa a kewayen ƙauyen.

Daga baya kuma waɗanda suka shiga aikin nema da ceto ne suka ɗauko gawar.

A ranar Lahadi ne aka kawo gawar tasa fadar, inda aka yi sallar jana’iza da kuma binne shi.

Ɗaya daga cikin masu riƙe da muƙaman gargajiya na ƙauyen ya tabbatar da faruwar lamarin.

Duk ƙoƙarin da aka yi domin samun tabbacin hakan daga Rundunar ‘Yan Sandan jihar ya ci tura, domin Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan, SP Ahmed Wakili, bai ɗauki waya ba, ko kuma amsa saƙon da aka aika ta wayar salula da ta WhatsApp a lokacin da aka buga labarin.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?