
Geng da Ummita
Mai Shari’a Sanusi Ado Ma’aji na wata babbar kotun jihar Kano da ke zamanta a Miller road Bompai, ya samu Frank Geng-Quangrong, ɗan ƙasar China da laifin kashe budurwarsa, Ummulkusum Sani Buhari (Ummita).
A watan Satumban 2022 ne Geng ya kai hari gidan Ummita kuma ya daɓa mata wuƙa har lahira a lokacin da suke jayayya.
Ya gudu daga wurin amma daga bisani ‘yan sanda sun kama shi kuma suka gurfanar da shi a gaban kuliya.
A lokacin da ake yi masa tambayoyi a kotu, ya ce Ummita ta yaudare sa ta hanyar yin aure da wani a yayin da yake shirin auren ta.
Geng ya ƙara da cewa, a lokacin da suka fara shirye-shiryen bikin aurensu, ya saya mata lefe na naira miliyan 1.5, kayan zaƙi da sauran kayan da za su saka a ranar aurensu, sai kuma ‘Asoebi’ ga ƙawayenta da kuma sabbin takardun kuɗi naira 700,000 na liƙi a ranar auren.
“Na je Sokoto ganin ‘yan uwanta inda na kashe naira 700,000.
“A ranar 13 ga Satumba, 2022, ta nemi wasu kuɗaɗe da za a yi amfani da su a gidan da take ginawa a Abuja amma ban ba ta ba saboda ba ni da kuɗi a lokacin.
“Tun daga lokacin, ta daina amsa kirana saboda a tunaninta na talauce.
Ya ce Ummita ta yaudare shi ta yi aure da wani amma ta ci gaba da neman kuɗi a wurinsa kuma akwai lokacin da ta zo Kano, kuma ta tabbatar sun haɗu.
Ya ce, “Baya ga maƙudan kuɗaɗen da na kashe mata, na kai ta wurare kamar Bristol Palace da Central Hotel don ta ci abinci.
“Na saya mata gida na naira miliyan 4, motar da ta kai naira miliyan 10. Naira miliyan 18 a matsayin jari don fara kasuwanci, kuma na kashe naira 500,000 na jakunkuna da takalma a sabon shagonta da les da zannuwa na naira miliyan 1 da wani gida a Abuja da ta fara ginawa.”
Ya ƙara da cewa ya saya mata kayan gwal da kuɗinsu ya kai naira miliyan 5, naira miliyan 6 da za ta je ta samo takardar shaidarta a Jami’ar Sakkwato da kuma naira miliyan ɗaya don sanya na’urar amfani da hasken rana a gidansu.
A ranar Talata ne alƙalin ya yanke wa Geng hukuncin kisa ta hanyar rataya.