Back

An yanke wa Dani Alves hukuncin ɗaurin shekaru huɗu da rabi a gidan yari kan fyade 

An samu tsohon ɗan ƙwallon Brazil Dani Alves da laifin yin lalata da wata budurwa tare da yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru huɗu da watanni shida a ranar Alhamis.

Hukuncin da wasu alƙalai uku suka yanke a wata kotun Barcelona ya biyo bayan shari’ar da aka shafe kwanaki uku ana yi a wannan watan. Alves, mai shekaru arba’in, ya musanta aikata ba daidai ba yayin shari’ar. Zai iya ɗaukaka ƙara kan hukuncin.

Kotu ta samu Alves ya yi lalata da wacce abin ya shafa da sanyin safiyar ranar talatin da ɗaya ga Disamba, 2022, lokacin da ta ce ya yi mata fyaɗe a wani ɗakin wanka na wani gidan rawa na Barcelona.

Masu shigar da ƙara na ƙasar sun nemi ɗaurin shekaru tara ga Alves yayin da lauyoyin da ke kare wacce take tuhuman shi ke buƙatar shekaru sha biyu. Lauyan nasa ya nemi a wanke shi, ko kuma idan aka same shi da laifin, a yi mai ɗaurin shekara guda tare da biyan Yuro dubu hamsin (fam dubu arba’in da uku) ga wacce abun ya shafa.

Alves ya kasance a gidan yari tun lokacin da aka tsare shi a ranar ashirin ga Janairu. An ƙi amincewa da buƙatarsa ​​na neman beli saboda kotu ta ɗauke shi a matsayin wanda zai iya guduwa. Brazil ba ta mayar da ‘yan ƙasarta idan aka yanke musu hukunci a wasu ƙasashen zuwa ƙasarta domin yanke musu hukunci a can ba. Wacce abun ya shafa ta shaida wa masu shigar da ƙara na jihar cewa ta yi rawa da Alves kuma da son rai ta shiga gidan wankan gidan rawan na dare, amma daga baya lokacin da ta ke so ta fita bai bar ta ba. Ta ce ya mare ta, ya zage ta, ya kuma tilasta mata yin lalata ba tare da son ta ba. Alves ya gyara kare kansa a lokacin binciken yayin da yake tsare, da farko ya musanta duk wani saduwa da ita kafin ya yarda da saduwa wanda ya ce da yarda ta. Ya ce ya daɗe yana ƙoƙarin kare aurensa da rashin amincewa da saduwan tun farko. A lokacin shari’ar, lauyan sa ya mayar da hankali kan ƙoƙarin nuna cewa Alves ya bugu lokacin da ya sadu da matar.

Shari’ar ta rushe tarihin Alves a matsayin ɗaya daga cikin manyan ‘yan wasan ƙwallon ƙafa. Alves ya lashe kofuna da dama tare da manyan ƙungiyoyin da suka haɗa da Barcelona da Juventus da kuma Paris Saint-Germain. Ya kuma taimaka wa Brazil ta lashe Copa Américas biyu da kuma ƙarfen zinare ta Olympics. Ya taka leda a gasar cin kofin duniya na uku, babban kambun ɗaya tilo da bai ci ba, a shekarar 2022. Ya buga wa Barcelona wasa daga 2008-16 kuma ya koma ƙungiyar a takaice a 2022. Har yanzu yana da wurin zama a kusa da birnin.

Ya kasance tare da kulob ɗin Pumas na Mexico lokacin da aka kama shi. Pumas ya yanke kwangilarsa nan da nan.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?