Back

Andreas Brehme, Fitaccen ɗan ƙwallon Jamus ya mutu 

Andreas Brehme, wanda ya zura kwallon da ta lashe gasar cin Kofin Duniya ta Jamus ta 1990, ya rasu yana da shekaru sittin da uku.

Abokiyar zaman Brehme, Susanne Schaefer ce ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce ya mutu “ba zato ba tsammani” a cikin dare sakamakon bugun zuciya.

Brehme ya buga wa ƙungiyoyin da suka haɗa da Kaiserslauntern da Bayern Munich da Inter, ya kuma yi wa Jamus ta Yamma da Jamus wasanni tamanin da shida. Ya shiga horarwa, musamman tare da Kaiserslauntern, daga shekara ta dubu biyu zuwa ta dubu biyu da shida.

Ɗan wasan bayan na cikin tawagar Jamus ta Yamma da ta yi rashin nasara a gasar cin Kofin Duniya a shekarar 1986 da Argentina, kuma ya ci bugun fanariti a minti na tamanin da biyar da ya yanke hukuncin ƙarshe a lokacin da ƙungiyoyin suka sake haɗuwa bayan shekaru huɗu a wasan ƙarshe a Italiya.

Mutuwar tasa ta zo ne ƙasa da watanni biyu da rasuwar Franz Beckenbauer, wanda ya horar da Jamus ta Yamma zuwa wannan nasarar a shekarar 1990, kuma ya lashe gasar a matsayin ɗan wasa.

Bayern ta wallafa a shafinta na X cewa “FC Bayern ta yi matuƙar kaɗuwa da mutuwar kwatsam na Andreas Brehme.

“Dangi da abokansa suna jimamin mutuwar gwarzon ɗan wasan na Jamus . Za mu ci gaba da tuna Andreas Brehme a koyaushe – a matsayin zakaran duniya har ma fiye da haka a matsayin mutum na musamman.

“Zai kasance a koyaushe cikin dangin FC Bayern. Ka huta lafiya, masoyi Andi!,”

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?