Back

APC ta yi gargaɗi yayin da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta karɓi wasiƙar rusa masarautun jihar 

Wata ƙungiya mai suna ‘Yan Dangwalen Jihar Kano (Masu yin zaɓe na Kano), ta rubutawa Majalisar Dokokin Jihar takardar neman a sake bitar dokar kafa ƙarin masarautu huɗu na Gaya, Rano, Ƙaraye, da Bichi da gwamnatin da ta shuɗe na tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ta yi.

Ƙungiyar ta kuma yi kira da a mayar da tsohon Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II.

Wannan kira na ƙungiyar ya biyo bayan kalaman da tsohon gwamna Rabiu Kwankwaso ya yi na cewa jam’iyya mai mulki ta New Nigeria People’s Party a Kano za ta sake duba matakin da Ganduje ya ɗauka kan masarautar Kano.

Sai dai da take zantawa da ‘yan jarida a ranar Laraba, jam’iyyar APC ta yi gargaɗi kan duk wani yunƙuri na kawo cikas ga tsarin masarautu na yanzu, kamar yadda Ganduje ya ƙirƙiro, tana mai cewa hakan na iya tayar da zaune tsaye a garin.

Jam’iyyar adawa ta shawarci gwamnan NNPP Abba Yusuf da ya yi taka-tsan-tsan don gudun kada a tura shi yin wani abu da zai iya shafar zaman lafiya da ake samu a jihar.

A ranar Laraba ne ’Yan Dangwalen Jihar Kano ta miƙa wa jaridar PUNCH kwafin wasiƙar ta mai kwanan watan Fabrairu 5, 2024, wadda ta aike wa Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano.

A cikin wasiƙar, wacce kuma aka kwafi wa Gwamnan Jihar Kano, Mataimakin Gwamnan Jihar Kano da Sakataren Gwamnatin Jihar, ƙungiyar ta ce, “Rushe masarautun tare da Sarkin Kano zai samar da haɗin kai, zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano da maƙwaftanta.

“Mun rubuta ne domin roƙo da kuma jawo hankalin masu girma ‘yan Majalisa ga dokar da take tafiyar da ƙarin sarakuna a Jihar Kano. Musamman, muna so mu nemi nazari da yiwuwar rusa ƙarin sarakuna da sashin dokan da ya kai ga ƙirƙirar ƙarin masarautu huɗu.

“Mun yi imani cewa haɗa kan masarautun su zama masarauta ɗaya zai haifar da haɗin kai da ci gaba ga al’ummar Kano. Wannan haɗin zai iya daidaita tsarin mulki da haɓaka al’umma mai haɗin kai don ci gaban kowane ɗan ƙasa.

“Mun amince da ikon da Majalisar Dokokin Jihar Kano ke da shi kan batun gudanar da masarautu. Sai dai kuma muna roƙon Majalisar mai girma da ta sake duba matakin tsige HRH Sanusi Lamido Sanusi daga karagar mulki. Imaninmu ya ta’allaka ne a kan cewa mayar da shi kan karagar mulki za ta samar da haɗin kai, zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano da ma maƙwabtanta.”

Kungiyar, yayin da ta bayyana Sanusi a matsayin “wani mutum ne da ake girmamawa sosai kuma mai faɗa a ji wanda ya nuna jajircewarsa wajen kyautata rayuwar al’ummar jihar Kano a tsawon mulkinsa na Sarki,” ta ce zai zama maslaha ga Kano baki ɗaya ta dawo da shi zuwa ga karagar mulki.

“A lokacin da yake mulki, ya yi aiki tuƙuru wajen inganta zamantakewa da tattalin arziƙi, ilimi, kiwon lafiya, da inganta rayuwar al’ummar jihar Kano.

“Cire HRH Sanusi Lamido Sanusi daga karagar mulki ya haifar da rarrabuwar kawuna da tashin hankali a tsakanin al’ummar jihar Kano, lamarin da ya haifar da tashin hankali a tsakanin al’umma.

“Cikin tawali’u muna kira ga masu girma ’yan Majalisar da su yi la’akari da wannan al’amari domin ci gaba da haɗin kan Jihar Kano. Yin la’akarin da kuka yi na wannan batu babu shakka zai yi tasiri mai ɗorewa a makomar al’ummarmu.

“Muna fatan za a yi la’akari da roƙonmu cikin mutunci a matsayin wani muhimmin al’amari kuma muna sa ran samun sakamako mai kyau da zai iya tasowa daga wannan muhimmin bita,” in ji kungiyar.

Sai dai Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar APC a Jihar Kano, Alhaji Ahmad Aruwa, ya bayyana kira ko buƙatar ƙungiyar a matsayin tatsuniya.

Ya ce, “Jam’iyyar APC ta ɗauki wannan gimbin a matsayin tatsuniya. Ta yaya wata ƙungiya ko ’yan siyasa za su yi zanga-zanga ko gaya wa gwamnati ta rusa masarautun?

“Gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ta samu nasarori da dama da suka haɗa da samar da sabbin masarautu.

“Jam’iyyar APC a matsayinta na jam’iyya ba ta damu ba domin gwamnatin jihar a ƙarƙashin tsohon Gwamna Ganduje ta yi abin da ya kamata ta samar da masarautu kuma mutane sun ga muhimmancinsu.

“Ya kamata a mutunta cibiyoyin gargajiya kuma ƙungiyar ba ta yi ƙorafi ko nuna rashin amincewa ba lokacin da aka ƙirƙiro masarautun.”

Aruwa ya ce idan har gwamnatin NNPP na son rusa sabbin masarautun to ya kamata ta fito ta faɗa maimakon ɗaukar nauyin “wasu sojojin haya da sunan ƙungiyar neman rusa sabbin masarautun.”

“Abin da Kano ke buƙata a yanzu shi ne zaman lafiya, ba wai wani abu da zai iya kawo rikici ga jihar da mazaunanta ba,” in ji Aruwa.

Sai dai da aka tuntuɓi Shugaban Jam’iyyar NNPP na Jihar Kano, Alhaji Hashimu Dungurawa, ya ce, “Kowa yana da hakki akan ra’ayinsa. Don haka ƙungiyar tana da hakki akan nata.”

A shekarar 2019 Gwamna Ganduje ya rattaba hannu kan wata doka da ta raba masarautar Kano gida biyar ta hanyar ƙirƙiro wasu sabbin masarautu huɗu.

Daga nan sai ya tuɓe Sanusi, wanda shi ne Sarkin Kano na 14 a watan Maris 2020 ya kuma kore shi jihar Nasarawa.

Wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji, ya fitar ta ce an tsige Sanusi ne saboda rashin mutunta doka da oda daga ofishin gwamnan jihar da sauran hukumomi, gami da ƙin halartar tarurrukan hukuma da shirye-shirye da gwamnatin jihar ta shirya ba tare da wani dalili na doka ba wanda ya kai cikakken rashin biyayya.”

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?