Back

Atiku ya ziyarci Ningi, ya ce bai kamata Majalisar Dokoki ta zama makami a hannun azzaluman gwamnatoci ba

Atiku da Ningi

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce domin ƙasar nan ta ci gaba, bai kamata cibiyoyin gwamnati, musamman ma Majalisar Dattawa, su zama makamai “a hannun azzaluman gwamnatoci” ba.

Atiku ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar nuna goyon baya ga Sanata Mai Wakiltar Bauchi ta Tsakiya, Sanata Abdul Ningi, a gidansa.

A kwanakin baya ne Majalisar Dattawa ƙarkashin jagorancin Sanata Godswill Akpabio ta dakatar da Ningi bisa zargin da ya yi na cewa Gwamnatin Tarayya na gudanar da kasafin kuɗi saɓanin wanda majalisar ta amince da shi.

Da yake jawabi a gidan Ningi, ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, ya yi nuni da cewa, “gaskiyar cibiyoyin gwamnati, musamman irin su Majalisar Dokoki, madubi ne na yadda ake tsarewa da kare maslahar talakawa a tsarin dimokuraɗiyya.”

Ya ci gaba da cewa fafutukar da Sanata Ningi ya tsinci kansa a ciki ci gaba ne na ganin cewa hukumomin gwamnati a Nijeriya ba su yi amfani da ƙarfin tuwo wajen zaluntan talakawan ba.

“Ba kwanan nan aka fara wannan fafutukar ba. An fara ne a lokacin mulkin soja, kuma ya zama wajibi hukumomin gwamnati, musamman ma Majalisar Dokoki, kada su zama makamai a hannun gwamnatoci azzalumai.”

“A ziyarar da muka kawo a yau mun zo ne domin mu nuna goyon baya ga Sanata Abdul Ningi da kuma isar da saƙo ga waɗanda suke ganin aikin gwamnati tamkar wani makami ne na zaluntar jama’a, cewa Sanata Ningi ba shi kaɗai ba ne a wannan gwagwarmayar.

“Haƙiƙa, ɗaukacin al’ummar Nijeriya da abokan Nijeriya a ƙasashen duniya suna goyon bayan yunƙurin mu na tsarkake ƙasar daga azzaluman mutanen da ke kan madafun iko,” inji Atiku.

Da yake mayar da martani, Sanata Ningi ya godewa Atiku da tawagarsa bisa wannan ziyara da suka kai masa da kuma yadda suka zaɓi tsayawa a ɓangaren talakawa.

“Gwagwarmayar da muke ciki a yau don tabbatar da cewa kowace jam’iyyar siyasa da ke kan karagar mulki da kuma wanda ke riƙe da muƙamin gwamnati, dole ne maslahar talakawa ya kasance mai matuƙar muhimmanci da kariya daga son rai na wani mutum ko mai muƙamin sa” inji shi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?