Back

Baƙuwar cuta a Zamfara: Adadin waɗanda suka mutu ya ƙaru zuwa 13

Adadin waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon wata baƙuwar cuta, wadda ta fi shafar yara da mata, a wasu al’ummomi a Jihar Zamfara ya kai 13.

Bincike daga asibitoci da majiyoyin gwamnati ya nuna cewa an samu adadin mutane 505 da suka kamu da cutar a ƙananan hukumomin Maradun, Shinkafi da Gusau.

Haka kuma bincike ya nuna cewa cutar ta bazu zuwa ƙananan hukumomin Isa da Zurmi na jihohin Sokoto da Zamfara.

An gano cewa an fara samun ɓarkewar cutar ne a ƙauyen Tsibiri da ke ƙaramar hukumar Maradun a watan Fabrairun bana.

Wata majiya da ta tabbatar da cewa Tsibiri na fama da cutar tun a wancan lokacin, ta ce, “Ya zuwa ranar Lahadi 12 ga Mayu, 2024, an samu rahoton mutuwar mutane huɗu, tare da samun mutum 228 da suka kamu da cutar, yayin da aka tura wasu 10 zuwa Cibiyar Yaƙi da Cututtuka ta Shehu Shagari da ke Gusau.

“Yawancin marasa lafiya da ke da ƙananan matsaloli sun sami magani kuma an sallame su daga Cibiyar Kula da Lafiya ta Farko (PHC) a Tsibiri.”

Hakazalika, a ƙaramar hukumar Shinkafi, an ruwaito cewa an gano cutar a ƙauyen Galadi a watan Afrilu, biyo bayan ƙorafe-ƙorafen zazzaɓi da ciwon ciki. Wani ma’aikacin lafiya a PHC da ke Shinkafi ya tabbatar da mutuwar mutane shida cikin sama da 100 da aka samu, inda aka tura sama da majinyata 60 da ke fama da munanan cututtuka zuwa Cibiyar Yaƙi da Cututtuka ta Shehu Shagari.

Ya ce, “Cutar da alama tana yaɗuwa, tare da ɓullar cutar a yankunan da ke makwaɓtaka da ita, yana ƙara nuna damuwa game da & daƙile ta.”

Don haka ya yi kira ga gwamnatocin jihohin Sokoto da Zamfara da su ƙara tura ƙwararrun likitocin zuwa yankunan da abin ya shafa domin shawo kan lamarin kafin cutar ta ɓulla zuwa sauran al’umma.

Musa Salisu, mazaunin Maradun, ya bayyana damuwarsa da cewa duk da har yanzu cutar ba ta isa garin Maradun ba, dole ne gwamnati ta ɗauki matakin kare yaɗuwar cutar.

Ya ce ci gaba da yawaitar ‘yan bindiga ya ƙara wani haɗari, lura da cewa Babban Asibitin Maradun na da rauni saboda kusancinsa da ‘yan bindigar.

Salisu ya ce irin wannan yanayi na iya hana mazauna wurin neman magani saboda fargabar hare-haren ‘yan bindiga.

A baya Gwamnatin Jihar Zamfara ta tabbatar da ɓarkewar baƙuwar cutar a ƙananan hukumomin Maradun, Shinkafi da Gusau. Kwamishiniyar lafiya ta jihar.

Dakta Aisha Anka, ta ce cutar ta haɗa da ciwon ciki, tarin ruwa, ƙara girman hanta da mafari, zazzaɓi da rauni saboda gurɓataccen ruwa.

Ta ce gwamnatin jihar ta kai rahoton faruwar lamarin ga Hukumar Hana Yaɗuwar Cututtuka ta Nijeriya (NCDC) kuma ta duƙufa wajen ɗaukar matakan gaggawa domin gano musabbabin cutar tare da daƙile ɓarkewar cutar.

Ta ƙara da cewa an aika da samfurori zuwa ɗaƙunan gwaje-gwaje a Legas da Abuja.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?