
Sanata Abdul Ningi
Sanata Abdul Ningi mai wakiltar Mazaɓar Bauchi ta Tsakiya a Majalisar Dattijai, ya mayar da martani kan iƙirarin da ya yi dangane da dokar kasafin kuɗin shekarar 2024.
A wata zantawa da ya yi da ‘yan jarida a ranar Litinin, Shugaban ƙungiyar Sanatocin Arewa ya ce a shirye yake a dakatar da shi daga Majalisar.
Ningi ya ƙara da cewa bai taɓa bayar da shawarar cewa Shugaba Bola Tinubu na aiwatar da kasafin kuɗi guda biyu ba ko kuma ya nuna son zuciya ga Arewa.
Ya ƙara da cewa ya yi maganarsa a matsayinsa na Sanata ba Shugaban Ƙungiyar Sanatocin Arewa ba, cewa babu shakka an tabbatar da cewa an ware naira tiriliyan 25 a cikin kasafin, inda ya ba da misali guda uku (kuɗi, aiki da wurin aiki) amma ya kasa tabbatar da wurin aikin sauran Naira tiriliyan 3 ɗin.
A halin da ake ciki kuma, ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Ondo ta Kudu, Jimoh Ibrahim, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta gurfanar da Sanata Ningi a gaban kuliya bisa laifin bada labarin ƙarya da kuma karya zaman lafiya a Majalisar Dattawa da kuma ƙasa baki ɗaya.
A ranar Lahadin da ta gabata ne fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata ikirarin da Sanata Ningi ya yi na cewa gwamnatin tarayya na gudanar da nau’i biyu na kasafin kudin 2024.
A cewar wata sanarwa da Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Bayo Onanuga, ya ce iƙirarin da Sanatan ya yi na cewa Majalisar Dattawan ta amince da naira tiriliyan 25 a matsayin kasafin kuɗin 2024 ƙarya ne, inda ya ƙara da cewa naira tiriliyan 28.7 ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da shi kuma ya sanya hannu a kai.
Fadar Shugaban Ƙasar ta kuma bayyana cewa ikirarin da Sanata Ningi mai wakiltar Bauchi ta tsakiya ya yi na cewa kasafin kuɗin 2024 ya saɓawa arewa “bai dace da shugaba mai matsayinsa ba.”
Onanuga ya ce Shugaban Ƙasar yana jagorantar gwamnati mai adalci ga kowane bangare a Nijeriya. Ya ƙara da cewa ta fuskar samar da kuɗaɗe, raba jari da ayyuka masu fifiko, dokar kasafi ta 2024 ba ta yi son kai ga wani ɓangare na ƙasar nan ba.