Kwamitin Ganin Wata a Saudiyya ya bayyana cewa ba a ga jinjirin watan Shawwal a Saudiyya a yau ba.
Sakamakon haka, watan Ramadan mai alfarma zai ci gaba har zuwa ranar 9 ga Afrilu, wanda zai ɗauki kwana 30 kenan. Don haka za a yi Ƙaramar Sallah ne a ranar 10 ga Afrilu.
Tun da farko, Kotun Ƙolin Saudiyya ta yi kira ga ɗaukacin al’ummar Musulmin ƙasar da su duba jinjirin watan Shawwal a yammacin ranar Litinin 29 ga watan Ramadan.
Ganin jinjirin watan Shawwal shine ƙarshen watan Ramadan mai alfarma da kuma farkon Ƙaramar Sallah. Lokaci ne na taro na farin ciki da buɗa baki tare da dangi da abokai.
Yayin da ainihin ranar ke bambanta dangane da ganin wata, ana sa ran Nijeriya za ta yi bikin Ƙaramar Sallar a ranar 10 ga Afrilun bana.