
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio
Shugaban Kwamitin Majalisar Dattijai kan Harkokin Yaɗa Labarai, Yemi Adaramodu, ya mayar da martani kan iƙirarin da Shugaban Ƙungiyar Sanatocin Arewa, Abdul Ningi, ya yi na cewa an yi ƙari a kasafin kuɗin 2024.
Ningi a wata hira da BBC Hausa ya yi zargin cewa ƙudirin kasafin kuɗin da ‘yan majalisar suka amince da shi ya sha bamban da abin da ake aiwatarwa, inda ya yi zargin cewa an yi ƙarin kusan Naira tiriliyan uku a kasafin kuɗin.
Da yake mayar da martani kan iƙirarin Ningi, Adaramodu ya ce babu wani ƙari a kasafin kuɗi da Majalisar Dattawan Ƙasar tayi.
“Kasafin kuɗin ƙasa takarda ce ta jama’a, wacce ke bayyana kuɗaɗen shiga da ake sa ran Nijeriya za ta samu da kuma yadda za ta kashe su.
“Majalisar Dattijai a ƙarƙashin jagorancin Sanata Godswill Akpabio ba ta da masaniya game da wani nau’in aiwatar da kasafin kuɗin 2024 da ya sha bamban da wanda aka amince da shi.
“Bayanin kasafin kuɗin da tsarin amincewa an yi su ne a idon jama’a, yayin da Shugaban Ƙasa ya amince dashi a wani bikin jama’a. Da an gabatar da duk wani zagon ƙasa a gaban Majalisar Dattawa, idan akwai shi,” inji Adaramodu yayin da yake kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu cewa babu wani ƙarin kasafin kuɗi a ko’ina.
“Kuma muna da yaƙinin cewa za a aiwatar da dokar kasafin kuɗi ta 2024 a ƙarƙashin tatstsauran sa idon majalisa,” inji shi.