Ɗan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Bashir El-Rufai, ya zargi gwamnan jihar, Uba Sani da yin watsi da nauyin da ya rataya a wuyansa ta hanyar ƙaurace wa jihar a kodayaushe yana shaƙatawa a Babban Birnin Tarayya (FCT).
Bashir ya kuma zargi Gwamna Sani, wanda abokin mahaifinsa ne, da kewaye kansa da wasu muƙarraban da ba su iya aiki ba da aka naɗa don goyon bayan siyasa.
Bashir ya ce a maimakon gwamnatin Uba Sani ta amince da gazawarta, sai ta kauce ta hanyar nuna rashin jin daɗi kan bashin da ta gada daga gwamnatin Gwamna El-Rufai.
A ranar Asabar da ta gabata ne Gwamna Sani a wani taro da aka yi a Kaduna, ya ce ya gaji bashin da ya kai dala miliyan 587, naira biliyan 85 da kuma bashin kwangila 115 daga gwamnatin El-Rufai, wanda hakan ya sa biyan albashin ma’aikata ya yi masa wahala.
Amma, a wani martani ga iƙirarin da gwamnatin jihar Kaduna ta yi ta wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X jim kaɗan, Bashir El-Rufai ya caccaki Gwamna Sani da tawagarsa, inda ya zarge su da rashin iya aiki, ƙarin farashin kwangila da kuma rashin canjin kuɗin ƙasar waje, yana mamakin dalilin da yasa suke ba da nauyin bashi a matsayin uzuri na rashin aikinsu.
Matashin El-Rufa’in ya rubuta cewa: “Waɗannan mutanen sun fahimci cewa ba su da ƙwarewa kuma kawai hanyar da za su rufe shirmen ita ce su kauce mata. Tun daga Gwamna da kullum yake kwana a Abuja zuwa ga ɗimbin mataimaka da ba su iya aiki ba waɗanda kawai aka ba su tukuici saboda dalilan siyasa.”
Akan bayanan bashi na jihar, ya amsa da cewa: “Shi ne Sanatan Kaduna wanda ya nema kuma ya amince da lamunin.”
Idan dai za a iya tunawa Gwamna Sani ya kasance Sanatan Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawa ta 9 kafin ya zama gwamnan jihar a zaɓen 2023.
Bashir ya ƙara da cewa, “Mutum zai yi tunanin cewa daga dukkan kason da FAAC ke bayarwa waɗannan wawayen sun canza su zuwa dala, bashi ne zai zama mafi ƙarancin matsalolinsu.
“Gwamnati mai ci a Kaduna tana gina ɗakin liyafa akan kuɗi naira biliyan 7 amma tana kokawa kan basussukan da gwamnatin da ta shuɗe ta bari.”