Back

Ba Mu Da Hannu A Kan Tashin Farashin Kayan Abincin – Dangote

Babbar Darakta a rukunin kamfanonin Dangote, Fatima Aliko Dangote, ta bayyana cewa rukunin kamfanonin Dangote ba shi da alhakin tashin farashin kayayyakin abinci da ake fuskanta a kasar nan.

A wata hira da Sashen Hausa na BBC, Hajiya Fatima ta ce kungiyar ta sayar da kamfanin sarrafa abinci shekaru biyar da suka gabata ga Olam Group da ke sarrafa abinci da kasuwancin noma a Najeriya.

Ta ce Olam a yanzu shi ne ke samar da fulawa, taliya, semolina, ta bayyana cewa duk wata fulawa da ake samu a kasuwanni ba kamfanin Dangote ne ke samar da ita ba.

“A cikin yarjejeniyar siyar da rukunin, an amince da cewa za su ci gaba da yin amfani da sunan mu wajen yin kayayyakin su, kuma da fatan nan da shekara mai zuwa za su daina.

“Don abubuwan da ake amfani da su, sukari, gishiri, da kayan yaji na Dangote kawai muke samarwa. Har ila yau, muna fatan za mu fara noman shinkafa nan gaba kadan ko kuma nan badi,” in ji ta.

Fatima ta kara da cewa ba su ji dadin yadda farashin ke hawa sama ba wanda har ya kai inda kamfanin ba zai iya magancewa ba, tare da fatan abubuwa za su daidaita nan ba da jimawa ba.

Da aka tambaye ta ko kafa na da shirin rage farashin, sai ta ce, “Ba mu da alhakin tashin farashin. Muna sayen danyen sukari da daloli daga Brazil; ba sa siyar mana da naira, har da danyen gishiri da kowane abu, wannan shine batun.” 

“Siminti ne kawai muke samun albarkatun shi a Najeriya. Amma sarkar sarrafata tana kan dala, manyan motocin da ke jigilar kayayyaki, gas, tayoyi, da kayayyakin gyara duk a kan dala muke siyo su.’’

Sai dai ta yi ikirarin cewa kamfanin bai san cewa ana siyar da siminti kan Naira dubu goma Sha biyar ba a kasuwanni, inda ta kara da cewa farashin 50kg zai kai kusan Naira dubu bakwai zuwa Nsirs dubu takwas, Hakan ya danganta da nisan wurin.”

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?