Back

Ba mu yi kasafin kuɗi naira biliyan 6 don ciyarwar Ramadan ba, inji Gwamna Yusuf

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya musanta kashe naira biliyan 6 wajen ciyarwar watan Ramadan a jihar.

Gwamnan da yake magana a shafinsa na X da safiyar Lahadi ya yi watsi da rahotannin a matsayin jita-jita, yana mai cewa gwamnatin sa ta yi kasafin naira 1,197,700,000 ne don shirin.

Rahotannin da ke cewa gwamnatin ta ware naira biliyan 6 domin gudanar da shirin ya haifar da fushi musamman a shafukan sada zumunta.

Gwamnan ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da su tabbatar da bayanai kafin su bayar da rahoto.

“A cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, na lura da shati faɗi da kafafen yaɗa labarai ke yaɗawa game da zargin gwamnatinmu na kashe kuɗi naira biliyan shida don shirin ciyarwar watan Ramadan.”

“Ina so in bayyana cewa ainahin adadin kuɗin da aka kashe a shirin shine naira biliyan ɗaya da miliyan ɗari da casa’in da bakwai da dubu ɗari bakwai.

“Ina shawartar kafafen yaɗa labarai da su tabbatar da cewa sun samu alƙalumansu game da ayyukanmu daga majiyoyin da suka dace ba tare da bayar da tabbaci ga masu shati faɗi ba,” inji shi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?