Back

Ba mu yi nadamar zaɓen Tinubu ba, inji Shugabannin Fulani

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu

A jiya ne shugabannin Fulani (Ardos) suka tunatar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu cewa sun amince da takararsa na Shugaban Ƙasa kuma suka zaɓe shi domin magance ƙalubalen da ke fuskantarsu a matsayinsu na al’umma.

Da suke jawabi yayin taron Ƙungiyar Haɗin Kan Fulɓe don Zaman Lafiya Da Ci Gaba na Ƙasa da na Shiyya-shiyya da aka gudanar a ranar Litinin a Abuja, sun kuma tunatar da shugaban alƙawuran da ya yi wa Fulani a ƙasar nan a lokacin yaƙin neman zaɓe.

A jawabinsa na buɗe taron, shugaban ƙungiyar, Arɗo Aliyu Liman Bobboyi, ya ce an ba wa Shugaba Tinubu laƙabin Barkindo na Arɗon Nijeriya a lokacin amincewar wanda wata hanya ce ta ƙulla ʼyarjejeniya da Fulaaku’ da shi.

A nasa ɓangaren, ko’o’dinetan ƙungiyar na Kudu-maso-Yamma, wanda shi ne Arɗo Abeokuta, Muhammad Kabir Labar, ya yi fatali da dokar hana kiwo a kewayen Babban Birnin Tarayya, Abuja, ba tare da yin tanadin wata hanyar ba.

“Ana sa ran duk wanda ke son ya karɓi ragama ko kuma ya haramta ya kira masu ruwa da tsaki a tattauna hanyar da za a bi.

“Dole ne kasuwancinmu ya kasance a wani wuri kuma sauran kasuwancin suna buƙatar kasancewa a wani wuri. Duk mun amince da hakan. Mu yi la’akari da kanmu kuma mu tattauna hanyar ci gaba. Ba mu kira da a yi rigima ba. Mu ’yan Nijeriya ne masu son zaman lafiya, kuma tun ranar farko muna bayar da gudunmawar ci gaban ƙasar nan,” inji shi.

Da aka tambaye shi game da batun Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF) da ta nuna nadamar zaɓen Shugaba Tinubu, ya ce ƙungiyar ba ta cikin wata ƙungiya da ke nadamar zaɓen Shugaban Ƙasa.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?