Back

Ba za a yi gagarumin bikin cikar gwamnatin Tinubu shekara ɗaya ba, inji Ministan Yaɗa Labarai

Ministoci a wurin taron

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce ba za a yi wani gagarumin biki a ranar cikar gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu shekera ɗaya ba.

Idris ya bayyana haka ne a taron manema labarai na ministoci a ranar Laraba a Abuja.

A cewar sa, matakin ya yi daidai da muradin Tinubu na yi wa ƙasa hidima, da kuma amfani da albarkatun ƙasa yadda ya kamata domin amfanin ɗaukacin ‘yan Nijeriya.

Ya ce, “Ba za a yi gagarumin biki a ranar cikar gwamnatin shekara ɗaya ba, ba za a yi biki ba, ma’aikata daban-daban ne za su gabatar da jawabai.

“Wannan ya yi daidai da tsarin gwamnatin Tinubu na tabbatar da amfani da albarkatun ƙasa yadda ya kamata don isar da ribar dimokiraɗiyya ga ‘yan ƙasa.

“Shugaban Ƙasa ya ba da umarnin bayar da bayanai masu amfani cikin gaskiya, kan lokaci, kuma a kai a kai.

“Ana sa ran ‘yan jarida su riƙa bayar da rahoto cikin gaskiya da riƙon amana, tare da kishin ƙasa. Maƙasudin kafafen yaɗa labarai shi ne sanar da jama’a da kuma neman bayanai daga gwamnati.

“Don haka, Ma’aikatar Watsa Labarai da Wayar da Kai ta ga ya dace a ko yaushe ta yi wa manema labarai da mutane bayanin abin da Gwamnatin Tarayya ke yi.”

Ministan ya buƙaci masu aikin yaɗa labarai da su yi aikin su da zurfin sanin ya-kamata da kishin ƙasa.

Ya nanata cewa, a wani ɓangare na Jawabin Ministoci, ministocin ma’aikatu daban-daban za su fara gabatar da jawabai kan ayyukan ma’aikatun su daga ranar 22 ga wannan watan na Mayu.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?