Back

Ba za mu biya ko sisi ga masu satar mutane a matsayin fansa ba, inji Gwamnatin Tarayya

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris

Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin cewa kada a biya masu garkuwa da mutane kuɗin fansa komai yawan matsin lamba.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ne ya bayyana haka yayin taron Majalisar Zartaswa ta Tarayya da aka gudanar a Aso Rock ranar Laraba.

Ministan ya ce gwamnati na aiki ba dare ba rana don ganin an mayar da waɗanda aka sace zuwa ga iyalansu.

A Kaduna, an kwashe ɗalibai da almajirai da malamansu aƙalla 200 daga ƙauyen Kuriga, sannan an yi awon gaba da wasu mutane 16 a Gonin Gora, dukkansu har yanzu suna hannun masu garkuwa da mutane.

Yayin da aka ce masu garkuwa da mutanen Gonin Gora su 16 suna neman kuɗin fansa naira tiriliyan 40 da motocin Hilux 11 da babura 150 domin a sako su, ba a ji komai daga waɗanda suka tafi da ɗaliban makarantar Kuriga ba.

Haka kuma a Sokoto an kama mutane 15 a ƙauyen Gidan Bakuso yayin da wasu mata kusan 50 aka ce mayaƙan Boko Haram sun sace a jihar Borno.

Da yake amsa tambayoyi daga ‘yan jarida a fadar gwamnati da ke Abuja, Ministan ya amince da ƙaruwar hare-hare a baya-bayan nan, inda ya ce gwamnati na sanya ido sosai kan lamarin, yayin da jami’an tsaro ke ɗaukar matakan da suka dace don daƙile su.

Idris ya ce: “Yanzu, gaskiya ne wasu daga cikin waɗannan suna faruwa. Mun ga abin da ya faru a Kaduna, a Borno, sannan a Sakkwato. Tabbas, gwamnati na sanya ido sosai ba wai kawai ta zuba ido ba, tana kuma tabbatar da cewa hukumomin tsaro na ɗaukar matakan da suka dace don ganin an dakatar da hakan sosai.

“Yanzu kamar yadda na faɗa, Shugaban Ƙasa ya ce wannan lamari ne da ba za a amince da shi ba, kuma gwamnati ba za ta amince da sace-sacen mutane ko duk wani nau’i na laifi. Muna ganin wannan yana faruwa kuma gwamnati na ɗaukar matakai masu inganci, da farko don daƙile hakan, da kuma dakatar da yaɗuwar wannan a fili.

Ministan ya ce Shugaban Ƙasar ya ba da umarnin cewa, a cikin gaggawa jami’an tsaro su tabbatar da cewa an dawo da duk waɗanda aka yi garkuwa da su lafiya, sannan kuma su “tabbatar da cewa ba a biya ko kwabo ba a matsayin kuɗin fansa.

“Don haka, yana da mahimmanci a jaddada cewa babu ko sisi, gwamnati ba za ta biya kowa ko sisi ba kuma gwamnati tana fatan cewa waɗannan yara da sauran mutanen da aka sace za a dawo da su ga iyalansu cikin aminci.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?