Back

Babban Bankin Najeriya ya fara sayar da dala ga ‘Yan Kasuwar Canji Kai tsaye

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da matakin siyar da kuɗaɗen ƙasar waje da darajarsu ta kai dala dubu ashirin ga kowane ɗan Kasuwar Canjin Kuɗaɗen Ƙasashen Waje (BDC) da ya cancanta a faɗin ƙasar.

Wannan dai na zuwa ne sama da shekaru biyu bayan da tsohon gwamnan Babban Bankin Ƙasa, CBN, Godwin Emefiele, wanda aka dakatar ya dakatar da siyar da kuɗaɗen ƙasashen waje ga ‘yan canji a wannan ɓangaren na kasuwar canjin kuɗi.

Babban bankin ya bayyana hakan ne a cikin wata sabuwar sanarwa da aka fitar ɗauke da sa hannun Daraktan Sashen Kasuwanci da Musayar Kuɗi, Hassan Mahmud, a ranar Talata.

Sanarwar mai taken, “Sayar da Kuɗin Ƙasashen Waje ga ‘Yan Kasuwan Canji domin biyan buƙatar dillalai na musayar da ba za a iya gani ba” ta ce an ɗauki matakin ne da nufin gyara kura-kuran da ake samu a ɓangaren dillalan kasuwar canji a Najeriya da kuma cike gibin da ake samu a farashin canji.

Ta ce za a sayar da wannan kason ne a kan kuɗi Naira dubu ɗaya da ɗari uku da ɗaya a kowace dala, wanda ke nuni da raguwar adadin kuɗaɗen da aka kashe a Kasuwar Canjin Kuɗi ta Najeriya Mai Cin Gashin Kanta (NAFEM) kamar ranar ciniki da ta gabata.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Bayan sauye-sauyen da ake yi a kasuwar canji, da nufin cimma daidaiton farashin canji na Naira, babban bankin Najeriya ya lura da ci gaban taɓarɓarewar farashin a kasuwar canji, wanda hakan ke shiga cikin kasuwan bayan fage da kuma ƙara faɗaɗa darajar kuɗin musaya.

“Don haka, CBN ya amince da siyar da kuɗaɗen ƙasashen waje ga ‘Yan Kasuwar Canji da suka cancanta domin biyan buƙatar musayar da ba a iya gani. Za a siyar da dala dubu ashirin ga kowane ɗan kasuwar canji akan kuɗi Naira dubu ɗari uku da ɗaya a kowace dala- (wanda ke wakiltar ƙaramin farashin musaya da aka aiwatar a NAFEM na ranar ciniki da ta gabata, kamar yau, ashirin da bakwai ga Fabrairu, 2024).

“Dukkan BDCs an yarda su sayar wa masu amfani a tazaran da bai fi kashi ɗaya cikin ɗari (1%) sama da farashin sayan daga CBN.”

Sannan kuma ta umurci BDCs da suka cancanta da su biya Naira zuwa Asusun Naira na Ajiyar Kuɗin Waje na CBN da aka keɓe, sannan su gabatar da tabbacin biyansu, tare da wasu takardu masu muhimmanci.

“An umurci dukkan BDCs da suka cancanta su biya Naira ga Asusun Naira na Ajiyar Kuɗin Waje na CBN da aka keɓe sannan su gabatar da tabbacin biyansu, tare da wasu takardu masu mahimmanci, don karɓan kuɗin a rassan CBN da suka dace ABUJA, AWKA, LAGOS da KANO,” in ji ta.

A yunƙurin da CBN ke yi na ceto faɗuwar darajar Naira, ya yi sauye-sauye da dama wajen magance faɗuwar darajar Naira, kamar bincike da kuma kawar da tarin kuɗaɗen ƙasashen waje, iyakance kuɗaden ƙasashen waje akan neman ilimi da magani a ƙasashen waje, ƙara ƙaramar hannun jari na BDCs, da kuma daƙile masu ɓoye kuɗaɗen ƙasashen waje don sayarwa a f

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?