Back

Babbar Kotun Tarayya ta dakatar da dawo da Sanusi a matsayin Sarkin Kano

A ranar Alhamis ne wata Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta bayar da umarnin hana Gwamna Abba Yusuf mayar da Khalifa Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.

A wata ƙara da Alhaji Aminu Bappa Dan Agundi (Sarkin Dawaki Babba) ya shigar gaban Alkali, Mai Shari’a A.M Liman, a ranar Alhamis, Kotu ta ba da umarnin a dakatar da aiwatar da Dokar Masarautar Kano ta shekarar 2024 (1445 A.H).

Mai Shari’a Liman ya bayar da umarnin cewa, “Hukuncin umarnin wucin gadi na wannan kotun mai girma da ta dakatar da yin aiki da Dokar Masarautar Jihar Kano ta 2024 (1445 A.H), ta shafi dukkan ofisoshi da cibiyoyi na dukkan Masarautu da aka ƙirƙiro a ƙarƙashin Dokar Masarautar Jihar Kano, 2019, (1441 A.H).”

Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar da Gwamna Yusuf ya sanar da sake naɗin Sarki Sanusi jim kaɗan bayan sanya hannu a kan Ƙudirin Dokar Masarautar Kano da aka yi wa kwaskwarima.

An gudanar da bikin rattaba hannu kan ƙudirin ne a gidan gwamnati tare da halartar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Honarable Ismaila Falgore, da sauran manyan hafsoshi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?