Back

Babbar Kotun Tarayya ta hana dakatar da Ganduje

Abdullahi Umar Ganduje

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Kano, ta hana dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Hukuncin ya zo ne a ranar Laraba bayan Ganduje ya shigar da ƙara gaban kotu yana neman a tabbatar da haƙƙinsa na ji ta bakin sa.

Waɗanda ake ƙarar sun haɗa da ‘yan sanda, Jami’an Tsaron Farin Kaya, Jami’an Tsaron Farar Hula, da wasu mutane tara.

A ranar 16 ga Afrilu, shugabannin jam’iyyar APC a gundumar Dawaki a ƙaramar hukumar Tofa ta Kano, sun dakatar da Ganduje bisa zargin cin hanci da rashawa.

Bayan haka, Kwamitin Ayyuka na Jam’iyyar APC na Jihar Kano ya soke dakatarwar tare da hukunta shugabannin gundumar.

Sai dai Usman Na’Abba, alƙalin Babbar Kotun Kano ya tabbatar da dakatarwar da aka yi a ranar.

A cikin umarnin da Babbar Kotun Tarayya ta bayar a ranar Larabar da ta gabata, kuma aka bai wa manema labarai a ranar Alhamis, A.M Liman, alƙalin Babbar Kotun Tarayya da ke Kano, ya ce bai kamata a aiwatar da dakatarwar ba har sai an saurari ƙarar da kuma yanke hukunci.

“Duk waɗanda ake ƙara, bayin su, ko wakilai an hana su aiwatar da shawarar da aka cimma yayin taron gaggawa na ‘yan jam’iyyar APC na Ganduje, wanda aka gudanar a gundumar Ganduje na Dawakin Tofa.

“An umurci dukkan jam’iyyu da su ci gaba da kasancewa a halin da ake ciki kafin taron gaggawa na ‘yan majalisar zartarwa na jam’iyyar APC na gundumar Ganduje, har sai an saurari ƙarar tare da yanke hukunci mai inganci,” inji Liman.

Daga nan ne alƙalin ya sanya ranar 30 ga Afrilu don sauraron ƙarar Ganduje.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?