Back

Babu fashin shirin baiwa ɗalibai rance- in ji Tinubu

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce babu gudu babu ja da baya kan shirin bawa ɗalibai rance da gwamnatin shi ta ɓullo da shi.

Tinubu ya bayyana hakan ne ta bakin wakilcin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, a lokacin da yake jawabi a taron saukar Karatu karo na takwas na Jami’ar Tarayya ta Oye Ekiti (FUOYE), a jihar Ekiti, inda aka yaye ɗalibai dubu shida da dari biyar da sittin da uku 6,563 da suka kammala karatun digiri daban-daban na jami’ar.

Tinubu ya ce, gwamnatin tarayya ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen inganta ilimi a ƙasar nan, ya Kara da cewa an amince da shirin ne tun a watan shida na shekarar da ta gabata a matsayin hanyar da za a tabbatar da damar samun ilimi mai inganci.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji ya yi kira ga jami’o’i da su yi bincike da za su samar da mafita ga ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.

An bada digirin girmamawa na jami’ar ga Jagoran Majalisar Dattawa,, Sanata Michael Opeyemi Bamidele, daktan shari’ar jama’a (honoris causa), Shugaban Kwamitin Majalisar Dattijai kan Kasafin Kuɗi, Sanata Solomon Adeola, daktan lissafin kuɗi (honoris causa), da Hon. Yusuf Adamu Gagdi, daktan kimiyyar siyasa (honoris causa).

Tinubu ya ce ɗaya daga cikin manyan tsare-tsare na gwamnatin APC shi ne bunƙasa ilimi, musamman na manyan makarantu.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?