Back

Badaru ya yi alƙawarin tallafawa Ƙungiyar ‘Yan Kasuwar Arewa

Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, tare da Ƙungiyar ‘Yan Kasuwar Arewa

Ministan Tsaro Mohammed Badaru Abubakar, ya ce zai tallafawa Ƙungiyar ‘Yan Kasuwar Arewa don bunƙasa kasuwancinsu.

Sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Henshaw Ogubike, ya fitar ta bayyana cewa Badaru ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin ƙungiyar ‘yan kasuwar Arewa ƙarƙashin jagorancin muƙaddashin shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Adam Hassan Ibrahim, a Ma’aikatar Tsaro da ke Abuja.

Ya yi nuni da cewa ƙungiyar ta bada goyon baya sosai a lokacin zaɓen ƙananan hukumomi da gwamnatin jiha da Majalisar Dattawa da kuma babban zaɓen Shugaban Ƙasa na 2023 inda APC ta lashe mafi yawan waɗannan zaɓukan.

Sakamakon haka, Ministan ya yi wa ƙungiyar alƙawarin tallafi da sanin cikakken goyon bayan ƙungiyar a lokacin zaɓen 2023.

Da yake magana game da mahimmancin ƙungiyar ga ci gaban ƙasa, Badaru ya yi alƙawarin bayar da tallafi ba tare da ɓata lokaci ba yana mai cewa: “Ni ɗaya daga cikin ku ne, don haka na fahimci ƙalubalen ku.”

Ya yi alƙawarin isar da saƙon fatan alheri da buƙatunsu ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Ƙungiyar ‘Yan Kasuwan Arewa wata ƙungiya ce ta duk wasu halaltattun ‘yan kasuwa a faɗin jihohin Arewa goma sha tara da kuma Babban Birnin Tarayya kuma babbar ƙungiyar masu rijista a Nijeriya.

Tun da farko, shugaban ƙungiyar, Alhaji Adam Hassan Ibrahim, ya taya Ministan murnar naɗin da aka yi masa, inda ya ce hakan ya dace.

Ya ce maƙasudin ziyarar ta su shi ne su zo su taya Ministan murna kan naɗin da aka yi masa da kuma ƙaddamar da koke-koke domin jin daɗin ‘yan ƙungiyar.

Don haka ya yi kira ga Ministan da ya ci gaba da tafiyar da ƙungiyar a cikin tsare-tsaren jin daɗin jama’a na Gwamnatin Tarayya.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?