Back

Bana son zama ubangida, inji El-Rufai

El-Rufa’i

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya ce ba ya son a yi masa kallon ubangida a Kaduna.

Da yake jawabi a wajen wani taron ƙarawa juna sani na manyan jami’an gwamnati a Jihar Borno, ranar Litinin, El-Rufai, ya ce sau biyar kacal ya ziyarci Kaduna tun bayan da ya bar mulki kusan shekara ɗaya da ta wuce.

“Ba na son zama ubangida, shi ya sa ba na tsoma baki a cikin abin da ke faruwa a Kaduna, ina son shi (gwamnan) ya koya kuma ya yi aikin da kansa.”

“Ya kamata shugaban ya samu mutanen kirki su yi aikin. Allah ne kaɗai zai iya yin komai da kanshi, duk iyawarka a matsayin shugaba, ba za ka iya yin tasiri kamar mutanen da ke kusa da kai ba.”

Wannan dai shi ne karon farko da El-Rufai zai yi magana a bainar jama’a tun makonni biyu da suka gabata lokacin da ɓaraka tsakaninsa da wanda ya gaje shi Sanata Uba Sani ta fara.

A wani taro da aka yi a garin Kaduna a ranar 30 ga Maris, 2024, Sani ya ce gwamnatinsa ta gaji bashin da ya kai dala miliyan 587, da naira biliyan 85, da kuma bashin kwangila 115 daga gwamnatin El-Rufai.

Gwamna Sani ya koka da yadda farashin canji ya tashi, yanzu jihar na biyan kusan sau uku na abin da gwamnatin da ta gabata ta karɓo.

Da yake bayyana cewa ɗimbin basussukan da ake bin jihar na cinye kason da Gwamnatin Tarayya ke bayarwa, ya ce an cire naira biliyan 7 daga cikin naira biliyan 10 da Gwamnatin Tarayya ta ware wa jihar a watan Maris domin biyan bashin jihar.

Gwamnan ya kuma koka da yadda aka bar jihar da naira biliyan 3, adadin da ya ce bai isa a biya albashi ba, domin kuɗin albashin jihar ya kai naira biliyan 5.2 duk wata.

Duk da cewa ɗaya daga cikin ‘ya’yan El-Rufai ya soki gwamnan, wanda ya zarge shi da rashin iya aiki, tsohon gwamnan ya ƙauracewa faɗin albarkacin bakinsa.

A halin da ake ciki kuma, yaƙin cacar baki tsakanin El-Rufai da magajinsa, ya haifar da tazara a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Kaduna yayin da masu ruwa da tsaki da magoya bayan jam’iyyar suka rabu a tsakanin ɓangarorin biyu.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?