Babban bankin Fidelity Plc ya raba kayan abinci sama da 3,000 ga gidaje masu rauni da iyalai marasa galihu a Gusau na jihar Zamfara.
Gudunmawar wata karamci ce a ƙarƙashin Ƙaddamar da Haƙƙin Jama’a na Bankin (CSR) wanda aka ƙirƙira don isa ga mutane masu rauni da kuma rage tasirin yunwa a cikin al’umma.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban bankin na shiyyar Arewa maso Yamma 2, Muhammad Ahijo, ya bayyana cewa “Shirin Fidelity na Abinci yana da nufin rage wahalhalun da mutane da dama ke fuskanta a halin yanzu na ƙalubalen tattalin arziƙin ƙasar nan.
Ya ce “A bankin Fidelity, mun fahimci muhimmancin tallafawa da ƙarfafawa al’umma don bunƙasa da ci gaba kuma mun yi imanin cewa ta hanyar saka hannun jari don jin daɗin al’ummomin da muke aiki a ciki, muna ba da gudummawa ga samar da al’umma mafi kyau ga kowa.”
“Mun yi imani da gaske cewa ta hanyar magance tushen talauci da rage yunwa, za mu iya yin tasiri mai ma’ana ga rayuwar masu buƙata. Kuma bisa la’akari da haka, bankin Fidelity ya ba da tallafin kayan abinci 3,000 ga iyalai marasa galihu a jihar, don taimaka musu su shawo kan wannan mawuyacin hali.”
Da yake yaba wa shirin na bankin Fidelity, Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, wanda Shugaban Ma’aikatansa, Alhaji Mukhtar Lugga ya wakilta, ya ce “Muna godiya da irin wannan karimcin da bankin Fidelity ya yi na bayar da tallafi ga gidaje masu rauni da kuma iyalai marasa galihu a cikin al’ummar mu. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da mutane ba sa iya sayan abinci kafin Ramadan da kuma lokacin watan Ramadan mai alfarma”.
A nasa ɓangaren, Akanta Janar na Jihar Zamfara, Alhaji Ali-Akilu Muhammad, ya gode wa bankin Fidelity bisa wannan karamcin da ya yi, ya kuma buƙaci sauran bankunan da ke aiki a jihar su yi koyi da bankin Fidelity ta hanyar bayar da tallafi ga iyalai marasa galihu a jihar.