Back

Bashin El-Rufa’i: APC ta dakatar da shugabar matan jam’iyyar ta jihar kan sukar Gwamnan Kaduna

Jam’iyyar APC reshen jihar Kaduna ta dakatar da shugabar matar jam’iyyar ta jihar, Maryam Suleiman, bisa zargin ta da aikata ba daidai ba.

Wasiƙar dakatarwa mai kwanan wata 31 ga watan Maris mai ɗauke da sa hannun shugaban jam’iyyar APC da sakataren gundumar Badarawa/Malali, Ali Maishago da Zakkah Bassahuwa, bi da bi, ta ce an dakatar da shugabar matan ne bisa zargin ɓata sunan Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna, da kuma yaɗa rikicin jam’iyyar ba tare da izini ba wanda hakan ya ɓata sunan gwamnan.

An kuma yi zargin cewa ta aika ‘yan daba su kai wa mai baiwa gwamna shawara kan harkokin siyasa, Manzo Maigari hari.

Wasiƙar ta nuna cewa matakin shugaban matan ya saɓawa Doka ta 21, 2 (v) na kundin tsarin mulkin APC.

Jam’iyyar ta ce dakatarwar ba za ta ƙare ba har sai an gudanar da bincike kan zargin. A wani faifan bidiyo da ta yi cikin harshen Hausa, shugabar matan jam’iyyar APC ta soki kalaman Gwamna Sani kan ɗimbin bashin da gwamnatin tsohon Gwamna Nasir El-Rufai ta bari.

A jawabin da ya yi wa masu ruwa da tsaki a taron da aka gudanar a ranar Asabar, Gwamna Sani ya ce ya gaji bashin da ya kai dala miliyan 587, da naira biliyan 85, da kuma bashin kwangila 115 daga gwamnatin El-rufai, lamarin da ya ce gwamnati mai ci ta kasa biyan ma’aikata albashi saboda cirewa daga kason gwamnatin tarayya.

Amma da take mayar da martani kan kalaman gwamnan, shugabar matan jam’iyyar APC ta wani faifan bidiyo da ta wallafa a shafukan sada zumunta, ta zargi gwamna Sani da rashin adalci tare da yi mishi gargaɗi da ya daina ɗora wa El-rufai laifin gazawarsa.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?