Back

Bayan biyan kuɗin fansa, ‘yan bindiga sun saki sojan sama, matarsa da ɗan uwansa har yanzu suna tsare

An sako wani shugaban cibiyar sarrafa jiragen yaƙin soji, Nurudeen Popoola, na Rundunar Sojojin Saman Nijeriya, wanda wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka sace shi a watan Disambar bara.

An ji cewa jami’in na Rundunar Sojojin Sama yana samun kulawa a wani asibiti da ba a bayyana ba.

An sace Popoola ne tare da matarsa, Ganiyat Olawale-Popoola, da ɗan uwansa, Abdulmumin Folaranmi a gidansu da ke kusa da Asibitin Ido na Ƙasa dake Mando a jihar Kaduna.

Wani ɗan uwa a farkon watan Fabrairun wannan shekara, ya roƙi hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da sakin waɗanda aka sace.

An samu labarin cewa an saki jami’in sojin saman bayan an biya wasu kuɗaɗe da ba a bayyana adadinsu ba.

Sai dai har yanzu masu garkuwa da mutanen ba su saki matar jami’in sojin saman da ɗan uwansa ba.

“Muna godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki da duk wanda ya goyi bayan wannan harka da ya ba ɗan uwanmu rai da kuma dawo da shi gida, har yanzu muna baƙin cikin cewa har yanzu matar sa da ɗanmu suna tsare a dajin Kaduna.

“Don Allah a taimaka mana mu ci gaba da yi wa sauran biyun da ke hannunsu addu’a domin a sako su cikin ƙoshin lafiya,” inji shi.

Dan uwan nasu ya tabbatar da sakin jami’in a ranar Juma’a.

Ya faɗa cewa; “An sake shi jiya. An kai shi asibiti. Amma ba a sako matar da dan uwan nasa da yake ɗalibi ba. Muna addu’ar Allah ya sa su ma su dawo,” inji shi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?