Back

Watanni biyu kenan, EFCC da Fadar Shugaban Ƙasa basu ce komai akan Edu, da Halima ba

Dakta Betta Edu

Watanni biyu bayan dakatar da Dakta Betta Edu, Ministar Harkokin Jin Ƙai da Yaƙi da Fatara, Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa, EFCC, da kuma fadar Shugaban Ƙasa sun jefa ‘yan Nijeriya cikin duhu kan mataki na gaba.

An ruwaito cewa binciken da aka yi ya nuna cewa bayan dakatarwar da EFCC ta yi wa Edu ranar 8 ga watan Janairu, sannan kuma ta yi cikakken bincike, ta miƙa wa fadar Shugaban Ƙasa rahoton wucin gadi.

An samu labarin cewa Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta miƙa rahoton wucin gadi na binciken da ta yi kan zargin da ake yiwa ministar da aka dakatar, inda ta bada shawarar a gurfanar da Edu a gaban kuliya.

Sai dai kuma idan aka yi la’akari da irin rawar da ta taka wajen samun nasarar jam’iyyar APC mai mulki, ana zargin wasu masu faɗa a ji ciki har da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, na ƙara matsin lamba ga Shugaba Bola Tinubu kan ya “sassauta” mata.

Majiyoyi sun ce masu goyon bayan masu tasiri suna roƙon cewa a sake ba wa Edu wani muƙami, ba lallai ne a mayar da ita muƙamin minista ba.

Akasin haka, an gano cewa Halima Shehu, Ko’odinetar Hukumar Kula da Zuba Jarin Jama’a ta Ƙasa (NSIPA) da aka dakatar, ta yiwu EFCC ta wanke ta a rahotonta na wucin gadi.

“Takardun da aka bankaɗo game da ƙuɗaɗen da NSIPA ta fitar a ƙarƙashin Halima, EFCC ta yi bincike akan su. An gano waɗannan kuɗaɗen sun bi ƙa’idodi saboda duk ɓangarorin da abin ya shafa sun amince da sa hannunsu.

“An gano cewa an fitar da kuɗaɗen ne saboda dalilan da aka ware su. Banda haka, Halima taci gaba da biyan kuɗaɗen ne daga inda magabaciyar ta ta tsaya. Kuma an yi hakan ne don gujewa shari’a, domin ‘yan kwangilar sun gabatar da takardar shedar nuna amincewarsu,” inji majiyar.

Wata majiya ta ce, “Amma wani mutum mai ƙarfi a fadar Shugaban Ƙasa bai ji daɗin rahoton na EFCC ba, don haka ya ce waɗanda suka kawo shi da su mayar da shi su sake duba rahoton”.

Amma da aka tuntuɓi don jin sahihancin iƙirari na cewa an miƙa rahoton wucin gadi ga Shugaban Ƙasa Tinubu, Dele Oyewale, Mai Magana da Yawu EFCC, ya shaida cewa har yanzu ana ci gaba da bincike kan lamarin.

Da aka tambaye shi lokacin da za a kammala binciken, la’akari da cewa majiya mai tushe ta tabbatar da gabatar da rahoton wucin gadi, Oyewale ya ƙi yin ƙarin bayani.

A nasa ɓangaren, lokacin da aka tuntuɓi zargin cewa Akpabio yana aiki tuƙuru don ganin an samu “sassauci” ga Ministan Jin Ƙai da aka dakatar, Eseme Eyiboh, wanda shi ne mai magana da yawun Shugaban Majalisar Dattawa, ya ce, “Betta Edu ba ta taɓa zama a majalisa ba, kuma ba Shugaban Majalisar Dattawa bane ya naɗa ta a matsayin minista.

“Na tuna cewa wanda ya naɗa ta ne ya dakatar da ita ba Shugaban Majalisar Dattawa ba. Babu yadda za a yi Shugaban Majalisar Dattawa ya iya yin tasiri a kan makomar kowane minista musamman Dakta Betta Edu,” inji mai baiwa Shugaban Majalisar shawara kan harkokin yaɗa labarai.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?