Back

Betta Edu: EFCC ta ƙwato naira biliyan 30, ana ci gaba da binciken asusun banki 50

Ministar Harkokin Jin Ƙai, Dakta Betta Edu

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), na binciken wasu asusun banki 50, yayin da ta ƙwato naira biliyan 30 a shari’ar da ake yi na Ministar Harkokin Jin Ƙai, Betta Edu, da aka dakatar, da kuma binciken ma’aikatar kan halasta kuɗaɗen haram.

Wannan sabon ci gaban ya fito ne a cikin wata sanarwa mai suna, “EFCC Alert,” wanda ke bayyana wasu manyan kame-kame, gurfanarwa gaban ƙuliya, da ƙwace-ƙwace da hukumar ta yi a cikin watan jiya.

Takardar da Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya ba da izini, wacce aka samu a ranar Litinin, ta bayyana cewa naira biliyan 30 da aka ƙwato na cikin asusun Gwamnatin Tarayya.

Takardar ta ce, “Ci gaba kan binciken Betta Edu. Muna da dokoki da ƙa’idoji da ke jagorantar binciken mu. Ƴan Nijeriya ma za su san cewa tuni aka dakatar da su, kuma hakan ya samo asali ne daga binciken da muka yi, kuma Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya tabbatar wa ƴan Nijeriya cewa a shirye yake ya yaƙi cin hanci da rashawa.

“Bugu da ƙari kuma, dangane da wannan lamari, mun ƙwato sama da naira biliyan 30, wanda tuni ke cikin asusun Gwamnatin Tarayya.

“Yana ɗaukar lokaci kafin a kammala bincike; mun fara wannan lamari ne ƙasa da makonni shida da suka gabata. Wasu lamurra na ɗaukar shekaru don bincike.

“Ya kamata ƴan Nijeriya su ba mu lokaci kan wannan al’amari; muna da ƙwararru kan wannan lamarin, kuma suna buƙatar yin abubuwa daidai. Akwai jagora da yawa nan da can.

“Kamar yadda yake a yanzu, muna binciken sama da asusun banki 50 da muka gano kuɗaɗen a ciki. Wannan ba wasan yara bane. Wannan babban al’amari ne. Sai ku yi tambaya game da ƙarfin ma’aikatana.

“Sannan kuma, muna da dubunnan wasu ƙararraki da muke aiki a kai. Ƴan Nijeriya sun ga tasirin abin da muka yi ya zuwa yanzu, ta yadda aka dakatar da wasu mutane kuma ta hanyar ƙwace-ƙwace da muka yi.

“Idan batun ganin mutane ne a gidan yari, to su jira. Komai yana da tsari da zai bi. Don haka ƴan Nijeriya su jira su yi mana uzuri.”

Hukumar EFCC ta kuma yi kira da a haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen yaƙi da cin hanci da rashawa, yayin da ta buƙaci ɓangaren shari’a da ƴan majalisa da su taimaka wa hukumar wajen yaƙi da cin hanci da rashawa.

Olukoyede ya ƙara da cewa, “Babu wanda zai iya yaƙin cin hanci da rashawa shi kaɗai. Don haka, muna son ƴan Nijeriya su yi imani da iyawarmu wajen wannan yaƙin. Dole ne kuma mu haɗa kai mu yarda cewa cin hanci da rashawa ba shi da kyau, don haka idan muna tuhumar masu cin hanci da rashawa, ƴan Nijeriya su yi imani da shi. Don haka dole ne mu yarda cewa abin da ba daidai bane ba daidai bane.

“Ina kuma kira ga sauran masu ruwa da tsaki – Majalisar Dokoki da kuma ɓangaren shari’a da su ba mu goyon baya a wannan aiki. Dole ne kowane ɗan Nijeriya ya zama mai yaƙi da cin hanci da rashawa. Idan kun ga wani abu ba daidai ba, ku yi magana. Ku ƙalubalanci gurɓatattun ƴan siyasa a yankinku. Ku tuhume gwamnoninku kan kason da suke karɓa. Ta yin haka, za ku tallafa wa yaƙi da cin hanci da rashawa.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?