Back

Binciken Ganduje: Ba na farautar kowa don siyasa, inji Gwamna Yusuf

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf

Gwamna Abba Yusuf na Jihar Kano ya ce kwamitocin bincike guda biyu da gwamnatinsa ta kafa ba wai don su farauci ‘yan adawar siyasa a jihar ba ne.

Abdullahi Ganduje, wanda ya rigaye Yusuf, ya ce binciken an yi shi ne don shi kawai, yana mamakin dalilin da ya sa aka taƙaita binciken kan lokacin mulkin sa kawai ba a tsawaita zuwa lokacin da Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya mulki jihar ba.

Amma da yake magana a lokacin da ya karɓi baƙuncin Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, a gidan gwamnati a wani ɓangare na ayyukan “Hawan Nassarawa” a ranar Juma’a, Yusuf ya ce an kafa kwamitin ne domin tabbatar da gaskiya da riƙon amana a cikin gwamnati da kuma shawo kan matsalar tashe-tashen hankulan siyasa a jihar.

Ya sha alwashin yin bincike tare da kamo waɗanda suke haddasa tashin hankali na siyasa, yana mai barazanar cewa gwamnati ba za ta ƙyale kowa ba, ba tare da la’akari da jam’iyyun siyasarsu ba.

A cewarsa, ana binciken ne don kawo ƙarshen tashin hankalin siyasa da ya haddasa asarar rayuka da asarar dukiyoyi domin ɗora jihar kan turbar ci gaban tattalin arziƙi da na siyasa.

Yusuf ya yi alƙawarin yin aiki kafaɗa da kafaɗa da masarautar yayin da ya bayyana irin gudunmawar da take bayarwa da kuma haɗin kai da gwamnati.

Yusuf ya ce tun lokacin da ya hau kan karagar mulki watanni 10 da suka wuce, gwamnatinsa ta fara yaƙi da dabar siyasa.

Gwamnan ya ce sama da ‘yan daban siyasa 200, da masu satar waya da Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta kama sun tuba kuma yanzu haka suna da amfani ga al’umma.

“Ba wata al’umma da za ta ci gaba ba tare da taimakon matasa ba; shi ya sa gwamnatinmu ta fi fifiko ga ci gaban matasa. Mun ɓullo da tsare-tsare daban-daban na ƙarfafawa matasa da mata, da nufin sanya su dogaro da kai.”

Yusuf ya ce, daga cikin abubuwan da suka sa a gaba a aikin kula da jihar akwai inganta harkokin kiwon lafiya, ilimi da ababen more rayuwa.

Ya ce tun daga lokacin da ya karɓi ragamar mulki, an inganta cibiyoyin kiwon lafiya a cikin birnin da sauran ƙananan hukumomi tare da samar da kayan aiki na zamani domin samar da ingantacciyar hidima. ”

Ana ci gaba da gina katafaren gadar sama na zamani guda biyu a cikin birnin, kuma burinmu shi ne mu mayar da Kano ɗaya daga cikin manyan biranen kasuwanci a faɗin duniya.

Ya ƙara da cewa gwamnatin sa ta kafa wani kwamiti da zai binciki laifuka da kuma satar kuɗaɗe da gwamnatin da ta shuɗe ta yi da nufin ƙwato kadarori da dukiyar al’umma da aka sace .

Tun da farko Sarkin Kano, Bayero, ya ce sun je gidan gwamnati ne domin yin mubaya’a a matsayin al’adar masarautar tsawon shekaru da dama.

Ya yaba da jajircewar Gwamna Yusuf na samar da ayyukan raya ƙasa masu abar yabawa waɗanda za su inganta rayuwar al’umma baki ɗaya.

Sarki Bayero ya buƙaci iyaye da su gaggauta ɗaukar matakin sanya ido kan inda ‘ya’yansu suke, domin daƙile illolin da ke tattare da zamantakewa da dabar siyasa.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?