Back

Boko Haram sun sake kai wa ‘yan gudun hijira hari a Borno, sun ƙona gidaje da dama

Wasu mutane da ake zargin ‘yan ƙungiyar Boko Haram ne sun lalata aƙalla sababbin gine-gine 25 waɗanda aka ware domin ‘yan gudun hijira da za su dawo a Ƙaramar Hukumar Dikwa ta Jihar Borno.

A lokacin da ake ta’addancin, mazauna Dikwa sun tsere daga gidajen su.

Kwanaki bayan sace ‘yan gudun hijirar da suka shiga daji neman itace, ‘yan ta’addan sun kai farmaki wani ƙauye mai nisa a Gajibo, inda suka yi ta harbe-harbe tare da ƙona sababbin gidaje sama da 25.

A cewar wani ganau, Modu Kundiri, wanda ke kan hanyar sa ta zuwa Maiduguri daga Gomboru, sojoji sun buƙaci su jira na tsawon sa’o’i uku a ƙauyen Logomani.

Ya ce: “Sojojin sun sanar da mu cewa sai mun jira na tsawon sa’o’i uku daga ƙarfe 11 na safe zuwa 2 na rana kafin a bar mu mu bar Logomani.

“Na gani kuma na ƙirga sababbin gidaje sama da 25 da aka gina a ƙauyen Gajibo da ke Ƙaramar Hukumar Dikwa.”

Wani mazaunin garin Dikwa, Sheriff Lawan, ya tabbatar da lamarin.

Ya ce ‘yan tawayen sun dasa bama-bamai da dama a wurin aikin gine-ginen domin daƙile ayyukan da gwamnatin jihar ke yi.

Ya ce: “Sojojin sun shaida mana cewa maharan sun dasa bama-bamai da dama a wurin da ake aikin kuma tuni sun gano wasu bama-baman.”

Garin Gajibo na da nisan kilomita 110 daga Maiduguri, babban birnin jihar.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?