
Kamfanin Access Holdings Plc ya sanar da naɗin Ms. Bolaji Agbede a matsayin Muƙaddashin Shugaban Kamfanin.
Kamar yadda Sanarwar da Sakataren Kamfanin, Sunday Ekwochi ya sanya wa hannu ta bayyana.
Hakan ya biyo bayan mutuwar tsohon Shugaban Kamfanin Dr. Herbert Wigwe a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu tare da matarsa, da ɗansa, da kuma tsohon Shugaban Kamfanin Musayar Kuɗi ta Najeriya, Abimboloa Ogunbanjo a ranar Juma’a a jihar California ta ƙasar Amurka.
Wata sanarwa da Hukumar Daraktocin Kamfanin ta fitar mai kwanan wata Sha biyu ga wannan watan, ta bayyana cewa naɗin ya dogara ne daga amincewar Babban Bankin Najeriya.
Ƙarin sanarwar da ta bayar mai kwanan wata Sha daya ga wannan watan, “Hukumar Daraktocin Access Holdings Plc (‘Kamfanin’) a yau na sanar da naɗin Ms Bolaji Agbede a matsayin Muƙaddashin Shugaban Kamfanin, biyo bayan mutuwar Tsohon Shugaban Kamfanin, Dr Herbert Wigwe, a ranar tara ga wannan watan.
I zuwa naɗin nata, Ms Agbede ita ce Babbar Darakta mai kula da tallafin kasuwanci.
Tana da kusan shekaru talatin na ƙwarewar aiki a cikin ayyukan banki da shawarwarin kasuwanci. Ta fara aikinta ne a cikin 1992 a bankin Guaranty Trust kuma ta yi ayyuka daban-daban a cikin ayyukan banki na kasuwanci da ayyuka da ta kai ga matsayin manaja a 2001.
Agbede ta shiga bankin Access ne a shekara ta dubu biyu da uku, a matsayin mataimakiyar babban manaja kuma tana da alhakin kula da harkokin bankin na kamfanonin kasuwancin sinadarai.
Ta zama shugabar ma’aikata ta bankin Access a shekarar 2010, inda take kula da ci gaban jarin dan Adam na kamfanin. Ta riƙe muƙamin har zuwa watan Yunin 2022 lokacin da aka naɗa ta a matsayin babban darektan Access Holdings bayan bankin ya sauya sheƙa zuwa kamfani mai riƙe da madafun iko.
Tsohuwar ɗalibar ta Jami’ar Legas ta fara aikinta a bankin Guaranty Trust (GTB), inda ta tashi daga jami’ar zartarwa a shekarar 1992 zuwa matsayin mai gudanarwa a shekarar 2001. Ta taɓa zama manajan dangantakar GTB kuma mai kula da ɗakin ajiya.
Daga baya Ms. Agbede ta yi aiki a matsayin Shugaban JKG Limited, kamfanin dake ba da shawara kan kasuwanci, a cikin shekara ta dubu biyu.