Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya amince da sayar da dala 10,000 ga kowane ɗaya daga cikin’ yan canji (BDCs) 1588.
A wata sanarwar da ya fitar da ke sanar da BDCs sabon matsayinsa, Bankin Ƙolin ya bayyana cewa za a sayar kan kuɗi naira 1,101 ga dala.
A cewar mai gudanarwa, ana sa ran BBDCs za su sayar da su a kan farashin da bai wuce kashi 1.5 sama da farashin sayarwa ba.
Naira na ci gaba da samun karɓuwa yayin da ta rufe a makon da ya gabata kan naira 1,251 bisa dala a kasuwa.