Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya umarci bankuna da su fara karɓar harajin kaso 0.5 na tsaron yanar gizo daga kuɗaɗen da abokan ciniki ke turawa.
CBN ya fitar da wata sanarwa a ranar Litinin, 6 ga watan Mayu inda ya ƙayyade cewa sabon harajin zai fara aiki makonni biyu daga ranar da aka fitar da sanarwar, wato Litinin 20 ga watan Mayu.
An ba da umarnin ga dukkan bankunan kasuwanci, ƴan kasuwa, marasa riba, da bankunan sabis na biyan kuɗi da masu gudanar da kuɗi ta wayar hannu da masu ba da sabis na biyan kuɗi.
Sanarwar ta ce, “Bayan zartar da Dokar 2024 ta aikata laifi ta yanar gizo (Hani, Rigakafi, da sauransu) (gyara) da kuma bisa tanadin sashe na 44 (2) (a) na dokar, harajin 0.5% 0.005) daidai da rabin kashi na duk ƙimar hada-hadar kuɗi ta yanar gizo ta kasuwancin da aka ƙayyade a cikin Jadawali na Biyu na Dokar’, za a tura shi zuwa Asusun Tsaro na Yanar Gizo na Ƙasa (NCF), wanda Ofishin Mai Ba da Shawarar Tsaro na Ƙasa (ONSA) zai gudanar.”
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Za a fara cirewa ne a cikin makonni biyu daga ranar da aka fitar da wannan sanarwar ga dukkan cibiyoyin hada-hadar kuɗi da kuma fitar da kuɗaɗen harajin da ake karɓa a duk wata zuwa asusun NCF da ke Babban Bankin CBN a rana ta biyar na kasuwanci a kowane wata.”
Waɗanda aka cire daga harajin sun haɗa da bayarwa da biyan lamuni, biyan albashi, tura kuɗi asusun ajiyar kuɗi a banki ɗaya ko tsakanin bankuna daban-daban na abokin ciniki ɗaya, tura kuɗi tsakanin abokan cinikin banki ɗaya.