Back

CBN yana bin ‘yan Nijeriya lamunin COVID-19 biliyan 261.07, inji rahoto

Wasu ‘yan Nijeriya da suka ci gajiyar lamunin Babban Bankin Nijeriya (CBN) da kuma cibiyar lamuni (TCF) ta Bankin NIRSAL sun kasa biyan naira biliyan 261.07 daga cikin naira biliyan 419.42 da aka bayar.

An ruwaito cewa cibiyar da aka ƙaddamar a watan Afrilun 2020 an yi ta ne don rage tasirin cutar ta COVID-19 akan gidaje da ƙanana da matsakaitan sana’o’i (SMEs).

A cikin takardar da CBN ta fitar, ta ce cibiyar ta haifar da samar da ayyukan yi 1,585,872, wanda hakan ya taimaka wa yanayin samun ayyukan yi a Nijeriya.

Ya ƙara da cewa, daga cikin naira biliyan 419.42 da aka fitar, manyan kuɗaɗen da aka biya sun kai kimanin naira biliyan 41.39, tare da kuɗin ruwa da ya kai kusan naira miliyan 174.60.

Sai dai akwai wani adadi mai yawa da ya kai kusan naira biliyan 378.03 da ba a biya ba, inda adadin kuɗin lattin biya ya kai naira biliyan 261.07, wanda hakan ke nuni da cewa ɗimbin masu karɓan ba su cika jadawalin biyan su ba.

Takardar ta bayyana cewa kowane ɗaya daga cikin manyan waɗanda suka ci gajiyar wannan rancen yana samun naira miliyan 2.5 ne domin kuɗin SME amma an kasafta shi a matsayin ‘marasa aiki’ wanda ke nuni da ƙalubale ko gazawa wajen biya.

Ɗaya daga cikin, Centriculture Limited, an lura da shi a matsayin ‘mai aiki’, tare da biyan naira miliyan 1.

Wasu shawarwarin da aka bayar a cikin takardar sun haɗa da amfani da tallafi ƙarƙashin Tsarin Zuba Jari na Sana’ar Noma/Ƙanana da Matsakaitan Sana’o’i (AgSMEIS) don ingantacciyar gudanarwa da sakamako.

Wata shawarar itace haɓaka dabarar fita wacce ta yi daidai da kuɗin da ake bi don taimakawa wajen rufe shirin cikin sauƙi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?