Asusun Kula da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), ta ce hare-hare da sace-sacen ‘yan makaranta a Nijeriya ya ƙaru tun bayan sace ‘yan matan makarantar Chibok a Jihar Borno shekaru 10 da suka gabata.
UNICEF, a cikin wani rahoto da ta fitar a ranar Litinin, ta ce kashi 37 na makarantu a jihohi 10 ne kawai ke da tsarin gargaɗin farko na gano barazanar irin waɗannan hare-hare.
Rahoton wanda Shugabar Hukumar UNICEF ta Nijeriya, Saadhna Panday-Soobrayan ta gabatar, ya yi la’akari da alƙaluma masu ban tsoro na tashe-tashen hankula da suka shafi yara.
A cikin shekaru 10 da suka gabata, an sace yara fiye da 1,680, an kashe 180 a hare-haren makarantu, sannan an yi garkuwa da ma’aikatan makaranta 60 tare da kashe 14. Bugu da ƙari, an kai hare-hare sama da 70 a makarantu, inji rahoton.
Ta kuma jaddada cewa har yanzu akwai ‘yan matan makarantar da aka sace su 90, kuma a baya-bayan nan ƙasar ta sake fuskantar wani sata yaran a Jihar Kaduna a watan Maris.
UNICEF ta yi kira ga hukumomi da su ƙara ƙaimi wajen kare yara masu rauni da inganta matakan tsaro a makarantu.
Wakiliyar UNICEF a Nijeriya, Ms. Cristian Munduate, ta bayyana buƙatar magance musabbabin matsalar, inda ta jaddada cewa ilimi wani haƙƙi ne mai muhimmanci ga makomar yara da kuma kawar da talauci.
Rahoton ya yi nazari kan fannoni shida da suka haɗa da tsarin makarantu, cin zarafin yara, haɗurran yanayi, tashe-tashen hankula, haɗurran yau da kullum, da kuma amintattun kayayyakin makaranta.