Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Neja, Shawulu Ebenezer Danmamman, ya ba wa iyalai 38 na jami’an rundunar da suka rasa rayukansu a bakin aiki tsakanin shekarar 2022 zuwa 2023 tallafin kuɗi naira miliyan 44.
Ya bayyana hakan ne a yayin taron ƙarshen wata da ya gudana a Ofishin ‘Yan Sanda da ke Minna, babban birnin jihar.
Ya ce an bayar da tallafin kuɗin ne ga iyalan da ke ƙarkashin Shirin Ƙungiyar Tabbatar da Rayuwa ta rundunar domin taimakawa iyalai da makusanta.
Kwamishinan ya kuma gabatar da wasiƙun yabo na NYSC ga jami’an hukumar su 17, waɗanda aka tura a matsayin tawagar ‘yan sandan da za su tabbatar da tsaro a sansanin NYSC na shekarar 2024 na Zangon A, Kashi na Ɗaya a Minna.
Ya ƙara da cewa, Ko’odinetan NYSC na jihar, Misis Abdulwahab Olayinka, ta yabawa tawagar bisa sadaukarwar da ta yi a yayin gudanar da atisayen, bayan da suka fuskanci ƙalubale masu tsanani.