Back

Cutar ƙyanda ta ɓulla yankunan Sharada, Gandun Albasa, da Madatai a Kano

Hukumomi a ƙaramar hukumar Kano Municipal ta jihar Kano sun tabbatar da ɓullar cutar ƙyanda a wasu sassan ƙaramar hukumar.

Ko’odinetan Kula da Lafiya na yankin, Alhaji Aliyu Jinjiri Kiru ne ya bayyana hakan a lokacin wani taro na Kwamitin Bayar da Agajin Gaggawa a sakatariyar ƙaramar hukumar.

Ko’odinetan ya ce yankunan da ake zargin sun kamu da cutar sun haɗa da Sharada, Madatai, da Gandun Albasa.

A cikin wata sanarwa da jami’ar yaɗa labaran yankin, Fatima Abdullahi ta fitar, ta ruwaito cewa Ko’odinetan ya ce sun samu rahoton ɓullar cutar ƙyanda da sauran cututtuka daga cibiyoyin kiwon lafiya da dama a ƙaramar hukumar.

Sai dai ya yi kira da a ɗauki matakin gaggawa don shawo kan cututtukan.

A nasa ɓangaren, jami’in kula da harkokin yaƙi da cututtuka, Tukur Hassan, ya ce tuni sun tura waɗanda abin ya shafa zuwa asibitin musamman na Murtala domin killace su.

Hakimin ƙaramar hukumar, Madakin Kano, Alhaji Yusuf Nabahani, ya yi kira ga dukkan masu unguwanni da su ba da fifiko kan harkokin kiwon lafiyar jama’a a kowani lokaci saboda muhimmancinsa.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?